Hukumomin ƙasar Turkiyya sun nemi al'ummar ƙasar da su ba da sunan da za a raɗa wa wani jaririn goggon biri da ƙaddara ta sa ya samu kansa ba zato ba tsammani a filin jirgin sama na Istanbul wanda aka yi fasa-ƙwaurinsa daga Nijeriya.
Ma'aikatar Noma da Harkokin Kula da Dazuzzuka ta Turkiyya ta wallafa sanarwar neman al'umma su ba da zaɓin sunan da za a saka wa jaririn goggon birin inda ta haɗa saƙon da maudu'in #BenceIsmi ko #MyNameOfChoice.
An gano goggon birin ɗan kimanin wata biyar ne a cikin wasu kaya da aka shigar da su ƙasar daga Nijeriya, waɗanda aka yi niyyar ratsawa da su ta Turkiyya ba tare da bin matakan da ake buƙata ba.
A ranar 22 ga watan Disamban da ya gabata ne Hukumar Kwastam ta Turkiyya ta ƙwace goggon birin, a ƙoƙarinta na daƙile fasa-ƙwaurin dabbobin daji ba bisa ƙa'ida ba.
Bayan ƙwacewar, sai aka miƙa birin wanda nau'insa ke ƙarewa a duniya, ga Ma'aikatar Noma da Harkokin Kula da Dazuzzuka, inda ake kula da shi da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Namun Daji ta ƙasar.
Ma'aikatar ta wallafa wani hoton birin mai tafe da saƙon da ke cewa: "Kar ku damu masu ƙaunata, ina nan lafiya."
Ta kuma ba da bayanai a kan halin lafiyar birin, tana mai cewa jaririn goggon birin yana lafiya kuma ana kula da shi.
Bayan da ta tabbatar goggon birin ya samu lafiya, sai ma'aikatar ta yanke shawarar shigar da al'umma cikin ɗaukar mataki na gaba a kan rayuwarsa - wato zaɓar masa suna.
"Muna neman sunan da za mu saka wa jaririn goggon birin. Don Allah ku gaya mana zaɓinku," in ji ta.
Jim kaɗan bayan saka sanarwar, sai maudu'in #BenceIsmi ya zama wanda ya fi tashe. Masu amfani da shafukan sada zumunta sun shiga lamarin inda suka dinga ba da zaɓin sunaye ga birin.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta ba da sunaye masu ma'ana da ma na nishaɗi.
Baya ga sunaye, ma'aikatar ta kuma samu saƙonnin da ke nuna goyon bayan kula da jaririn birin.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun nuna damuwa kan fasa-ƙwaurin namun daji tare da jinjina wa hukumomi kan ƙoƙarinsu na kare irin wadannan halittu da ke ƙarewa a duniya.
Son sanya wa jaririn birin suna na zuwa ne a wani ɓangare na shirin da ma'aikatar ke yi don kare namun daji da wayar da kan jama'a a kan barazanar da ke tattatare da ƙarewar namun daji.
Ma'aikatar ta kuma sake jaddada batun kula da birin, da ƙoƙarin mayar da hankali kan tabbatar da lafiya da tsaronsa har a can gaba.