Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa, kasar ta yi nasara a kan ƙungiyar 'yan ta'addan Daesh, wadanda a "baya-bayan nan aka yi yunkurin sake dawo da ita a matsayin wata ƙungiya ta yanki."
Turkiyya ta samu "gagarumar nasara ta ɓangaren kawar da ta'addanci daga tushensa," in ji Erdogan a ranar Lahadi a babban taron Jam'iyyar AK na lardin Trabzon karo na 8.
Ya ce, Turkiyya ta daƙile faɗaɗar kungiyar ta'addanci ta PKK daga kan iyakar kasar sakamakon ayyukan yaki da ta'addanci da Ankara ta gudanar, inda yake bayar da misali da kungiyar ta'addanci ta YPG/PKK,
"Babu shakka za mu cim ma burinmu na samar da ƙasar Turkiyya wadda rikici da tarzoma da rashin zaman lafiya za su zama tarihi a cikinta ta hanyar haɗin kai da taimakon juna," kamar yadda ya sha alwashi.
“Yanzu zamani ya wuce na dogaro da makamai da rikice-rikice da ta'addanci, da kuma turka-turkar da masu mulkin kama-karya ke mara wa baya,” in ji shi.
"Ba za mu bari a gina sabuwar katanga tsakaninmu da 'yan uwanmu maza da mata ba waɗanda muke zaune a wuri ɗaya da su tsawon dubban shekaru," in ji Erdogan.