Erdogan ya samu kuri'un da aka kiyasta yawansu da miliyan 27.5, inda ya tsere wa Kilicdaroglu wanda ya samu kuri'a miliyan 25 da sama da miliyan biyu. / Hoto: AA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya zamo shugaban da ya fi kowa dadewa a mulki bayan da ya fafata da abokin hamayyarsa, Kemal Kilicdaroglu, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

Sakamakon farko ya nuna cewa Erdogan ne a kan gaba da kashi 52.11 na jumullar kuri'un inda ya fi abokin hamayyarsa Kilicdaroglu, wanda ya samu kasa da kashi 48 a zaben da ake gani a matsayin wanda aka fi fafatawa tun bayan rushewar Daular Usmaniyya a Turkiyya.

A jawabin samun nasara da ya yi a hedikwatar Jam'iyyar AK da ke birnin Istanbul, an ga Erdogan cike da farin ciki yana rero baituka a wata shahararriyar wakar Turkiyya ga dubban magoya bayansa da ke wajen.

"Mun kammala zagaye na biyu na zaben shugaban kasa cikin goyon bayan mutane. Ina gode wa dukkan wadanda suka kada kuri'unsu," ya ce, yana mai karawa da "An dora mana nauyin kara shugabanci na wasu shekara biyar din."

Erdogan ya samu kuri'un da aka kiyasta yawansu da miliyan 27.5, inda ya tsere wa Kilicdaroglu wanda ya samu kuri'a miliyan 25 da sama da miliyan biyu.

Shugaban hukumar koli ta zaben kasar YSK zai sanar da sakamakon zaben a ranar 1 ga watan Yuni.

Nasarar Erdogan ta ba da mamaki matuka saboda yadda ya tsallake duk wata farfaganda da kafafen watsa labaran kasashen Yamma suka dinga yadawa a kansa.

Valeria Giannotta, Daraktar da ke sa ido kan Turkiyya a wata cibiyar bincike kan siyasar duniya da ke Italiya, ta bayyana Erdogan a matsayin "jajirtaccen shugaba kuma mai karfi", a wani sharhi da ta yi bayan kammala kada kuri'a.

“Sakamakon zaben ya nuna cewa 'yan Turkiyya sun fi son Erdogan da kuma ci gaban da yake wakilta... Za a sanya shekara biyar masu zuwa a matsayin na ci gaban ayyukan da aka fara, da suka hada da magance matsalar tsaro da yaki da ta'addanci.

"Ina sa ran ganin Turkiyya ta zama mai karfin kawo zaman kafiya a yankin," kamar yadda ta shaida wa gidan talabijin na TRT World.

Zagaye na biyu na zaben da aka yi shi ne irinsa na farko a tarihin kasar, saboda gaza samun dan takarar da ya samu kashi 50 a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka yi ranar 14 ga watan Mayu.

A wata sanarwa da Hukumar Koli ta Zaben Kasar YSK ta fitar bayan kammala kada kuri'a, shugaban hukumar ya ce an gudanar da zaben lami lafiya kuma ba a samu wani rahoto na samun cikas ba.

A zaben majalisar dokoki, Kawancen Al'umma da Jam'iyyar AK ta Erdogan ke jagoranta ne ya samu kaso mafi yawa inda ya ci kujera 323 a cikin 600 na katafariyar majalisar dokokin kasar.

Kiyasin da aka yi da farko na zagaye na biyun ya nuna cewa fiye da kashi 85 cikin 100 ne na yawan mutane da za su fita kada kuri'a, wato kadan cikin yawan wadanda suka fita a zagayen farko mai kashi 88.92. Yawan wadanda suka kada kuri'a daga kasashen waje kuma a wannan karon kashi 55.62 wanda ya haura zagaye na darko mai kashi 52.69.

Akwai mutum miliyan 64 da suka cancanci kada kuri'a daga cikin Tukiyya da kuma mazauna kasashen waje.

Da wannan nasara, Recep Tayyip Erdogan zai sake mulkar kasar har tsawon shekara biyar. An fara zabarsa a shekarar 2014 aka kuma sake zabarsa a 2018.

Shugaban mai shekara 69 ya kuma yi firaminista daga shekarar 2003 zuwa 2014. Sannan ya taba rike mukamin magajin garin birnin Istanbul daga 1994 zuwa 1998.

Da safiyar Lahadi ne Erdogan da matarsa Emine Erdoga suka kada kuri'unsu a Istanbul tare da yin kira ga 'yan kasa da su fita su yi zabe ba tare da jin ko dar ba.

A jajibirin zaben, shugaban ya yi kira ga magoya bayansa a Istanbul da su fita zabe, yana mai cewa mutum miliyan 85 'yan kasar Turkiyya ne za su yi nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

“Dukkan wadanda suke da yakini ga ci gaban kasa, suna da buri mai kyau ga kasar kuma za su ji cewa kasar za ta yi nasara a zaben 28 ga watan Mayun.

Fiye da mutum miliyan 64.1 aka yi wa rajista don kada kuri'a, da suka hada da miliyan 1.92 da suka fara kada kuri'unsu daga kasashen waje daban-daban.

An samar da akwatunan zabe sama da 192,000 a fadin Turkiyya.

An rufe rumfunan zabe a kan iyakokin kasashe ranar Lahadi, yayin da aka kammala zabe a ofisoshin jakadancin Turkiyya ranar 24 ga watan Mayu.

TRT World