Hukumar Koli ta Zabe, YSK ita ce hukumar kasar Turkiyya da za ta jagoranci gudanar da zaben kasa a ranar 15 ga watan Mayu /Hoto: AA

Gwamnatin Turkiyya tana aikin tabbatar da cikakken tsaro kafin, da kuma lokacin zaben kasar da zai gudana ranar 14 ga watan Mayu, zaben da ake gani a matsayin mafi muhimmanci a tarihin kasar.

Hukumar Zabe ta Koli (YSK) - hukumar zabe mafi girma a kasar - za ta sanya idanu da kula da gudanar da tsarin dimukradiyya mai girma har zuwa a kammala kirga kuri'u tare da sanar da wanda ya yi nasara.

A lokacin da ake ci gaba gangamin neman kuri'a, masu zabe sun shirya zaben shugaban kasarsu na nan gaba tare da 'yan majalisun dokoki, mun yi bayani kan hanya mai rikitarwa da ake bi don tabbatar da ingantaccen zabe kuma sahihi a Turkiyya.

Tsaro da zaman lumana

A fadin Ma’aikatar Cikin Gida ta Turkiyya, ranar zabe, kusan jami’an tsaro 600,000 ne za su yi aiki cikin larduna 81, don tabbatar da tsaro ranar zabe.

Jami’an tsaron sun kunshi ‘yan sanda 326,387, da jandarma 196,197, da jami’an kan-iyaka 7,000, da ‘yan masu gadi 58,658, da kuma ‘yan sintirin sa-kai 17,209.

Har ila yau, akwai tsarin kyamarorin tsaro da aka kafa a wurare na musamman, don sanya ido kan masu iya kawo cikas ga zaben.

Kamar dai a zabukan da suka gabata, za a saka ido kan abin da kyamarorin suke dauka game da zabukan, kuma a yi nazarin su kai-tsaye a Cibiyar Kula da Tsaron Zabe, karkashin Hukumar Tsaron Bai-daya, wadda ke ofishin ‘yan sanda mai hedikwata a Ankara.

A zaben kasa da ya gabata, sama da kyamarori 50,000 ne suka samar da hotuna da bayanai ba kakkautawa, daga bakin tituna, da fitattun hanyoyi, da kuma inda mutane ke bi zuwa tashoshin zabe.

Jami’an da ke kula da cibiyar, za su fara aiki tun safiyar ranar zaben har zuwa lokacin da za a kirga kuri’ar karshe don kammala aikin zaben.

A wani bangare na tsarin samar da tsaro, an haramta sha da siyar da barasa a wuraren taruwar jama’a a ranar zabe, daga karfe 6 na safe zuwa tsakar dare.

Babu wanda za a bari ya rike makami kamar bindiga, da abinyanke-yanke ko abin duka, idan ban da jami’an da ke da alhakin samar da tsaro.

Masu sa-ido daga kasashen waje

Wakilai daga kungiyoyin duniya daban-daban za su sa ido kan zabukan watan Mayu, bayan samun gayyata daga gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdogan. Wannan al’ada ta fara ne tun a shekarar 2002.

Akwai wakilai daga Hukumar Turai ta Security and Co-operation in Europe (OSCE), da kungiyar Shanghai Cooperation Organisation (SCO), da majalisar Parliamentary Assembly of the Council of Europe (PACE).

Sannan akwai wakilan kungiyar Parliamentary Assembly of the Mediterranean (PAM), da mutum biyar daga majalisar Parliamentary Assembly of the Black Sea Economic Cooperation (PABSEC).

Sauran su ne wakilan Parliamentary Assembly of Turkic-Speaking Countries (TURKPA), da kungiyar Organisation of Turkic States, wadanda suka yi aiki a matsayin masu sa-ido ‘yan ba ruwanmu a zabukan da suka gabata.

A lokacin zaben shugaban kasa da ‘yan majalisu na 2018, wakilan kasa-da-kasa na kungiyar OSCE sun kunshi masu sa-ido 330 daga kasashe 44, har da 231 da ‘yan sa-ido masu jimawa da marasa jimawa.

A cewar jami’an sa-ido na kasashen waje, duka zabukan da aka gudanar a Turkiyya tun shekarar 2002, sun kasance sahihai, masu ‘yanci, masu yalwar shiga, da adalci daidai da kwawawan tsarin da aka amincewa a duniya.

Kirga kuri’u

A zabukan baya-bayan nan, an yi amfani da akwatunan zabe 188,000 a lardunan zabe guda 87 a fadin kasar, da kuma kasashen waje, kamar yadda hukumar zabe ta tanada.

Bayan ‘yan kasa sun kada kuri’a kuma an rufe tashoshin zabe, aikin kirga kuri’a zai fara a bainar jama’a, karkashin jagoran akwatin zabe, tare da tallafin wakilai daga duka jam’iyyun siyasa da suka shiga zaben.

Jagoran akwati ne zai bude kowane akwati a gaban mahalartan da ke tashar zabe, da kuma ambulan masu kunshe ta kuri’un da aka aiko na mutane. Daga nan ne jagoran zai za a kirga da murya a bayyane.

Sannan sai wakilan jam’iyyu za su rattaba hannu kan takarda bayan su duka sun amince da sakamakon.

Ba za a dauke akwatunan zabe daga tashar zabe ba har sai an kammala kirgawa da rubuta sakamakon akwatunan zabe a duk fadin kasar.

Za a kirga da sahale duka takardun kuri’u sahihai, sannan a zayyana a jadawali. Kuri’un da ba sahihai ba, da wadanada aka yi jayayya a kai, da kuma ambulan da ba a yi aki da su ba, za a kunshe su daban, a sanya su a jaka da amincewar wakilan, sannan kwamiti ya daure su.

Ba tare da bata lokaci ba, akalla mutum biyu daga wakilan za su kai daurarrun jakunkunan wajen jagoran majalisar lardin zabe, tare da taimakon jami’an tsaro.

A karshe, majalisar lardin zabe za ta tattara duka sakamakon zabe da aka samo daga kwamitocin akwatunan zabe, sannan a sanar da shugabancin majalisar zabe ta yanki, da kuma jam’iyyun siyasa game da sakamakon.

Zabe a yankunan da girgizar kasa ta shafa

Daya daga cikin manyan kalubalen da ke gaban Hukumar Koli ta Zabe shi ne tabbatar da masu kada kuri’a a yankunan da aka yi girgizar kasa a ranar shida ga watan Fabrairu, sun shiga wannan zabe da tare da wani cikas ba.

Cikin makonnin da suka wuce, wakilai daban-daban na YSK sun ziyarci yankin da girgizar kasar ta shafa, don fayyace yanayin da ake ciki, da kuma sanin me ake bukata don samun nasarar zaben.

Tawagar da ta kai ziyarar tana rubuta rahotonta kan adadin masu zabe da abin ya shafa, da tantance wadanda aka kwashe su zuwa wasu yankunan, da kuma shirya irin tsaron da yankin yake bukata a halin yanzu.

A yanzu haka wannan aiki yana gudana, kuma ana aika rahotanni zuwa ga ofishin YSK.

A cewar rahotannin hukuma, ana yin kokarin samar damar yin zabe a garuruwan tantuna da kwantenoni. Haka nan ana duba yiwuwar kafa tashoshin a wannan garuruwa.

Wadanda girgizar ta shafa da suke jinya, kuma ba za su iya yin zabe ba, sannan suke fuskantar matsala wajen zirga-zirga, ko suka kasa tafiya saboda tsufa, za a ba su zabin yin zabe a tasoshin tafi-da-gidanka.

Ana kuma duba wasu tsare-tsaren na sauya wajen yin zabe zuwa inda ya fi kusa, a yankunan da ba za a iya yin zabe ba.

‘Yan kasa da suka batar da katin shaidarsu, sakamakon girgizar kasa, su ma za su iya kada kuri’a ba tare da katin shaidar ba, matukar suna da wasu takardun tantancewa, kamar katin shaida na wucin-gadi, ko fasfo, ko satifiket din aure, ko na tukin mota, ko na aikin soji, ko na kungiya ta musamman.

Haka wadanda girgizar kasa ta shafa za su iya zabe a garuruwan da da aka kai su bayan afkuwar lamarin.

Haka nan, ana sa ran za a fitar da umarnin doka da zai ba da dama ga jami’an kungiyar jin-kai ta AFAD don su iya yin zabe a garin da suke aiki a halin yanzu.

TRT World