Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya jaddada cewa dole ne Turkiyya da Girka su magance matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar da ta dace ba tare da sa hannun wasu ɓangarori daga waje ba.
Da yake jawabi a ranar Asabar ga Taron Kafofin Watsa Labarai na Turkiyya da Girka da aka gudanar a Istanbul, Altun ya bayyana cewa, "Dole ne ƙasashen yankin irin su Turkiyya da Girka su warware matsalolinsu bisa tsarin fahimtar juna da muradun ƙasa, ba tare da neman jagorancin wasu daga waje ba."
Ya ƙara da cewa, "Hakan ne ya sa tsare-tsaren kasuwanci da Turkiyya da Girka suka gabatar ke da matukar ma'ana."
Daraktan Sadarwar ya kara da cewa, ziyarar da Firaiministan Girka Kiryakos Mitsotakis zai kai Turkiyya ranar Litinin wata muhimmiyar dama ce ta ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu.
Da yake bayyana cewa Turkiyya a shirye take ta goyi bayan ga duk wani yunƙuri da zai ƙarfafa alaƙa da Girka, Altun ya tabbatar da cewa Ankara za ta ci gaba da riƙe wannan matsayi a nan gaba, ta hanyar kafa "kyakkyawar alaƙar maƙwabtaka da bunƙasawa da faɗaɗawa da samar da ƙarin hanyoyin tattaunawa."
Da yake jan hankali cewa Turkiyya da Girka suna ɗaya daga yankunan mafi fuskantar ƙalubale a duniya, Altun ya tunatar da cewa da farko dai ƙasashen biyu makwaɓta ne da kusancinsu da juna ke tasiri wajen alaƙarsu.
A jawabin nasa ga taron a ranar Asabar, Altun ya ƙara jaddada cewa, ƙasashen yankin "abin takaici, ba su da wani tasiri kuma suna sanyin jiki a siyasance" a abubuwan dake faruwa a duniya a yanzu.
"Muna rayuwa ne a lokacin da wajibi ne ƙasashe masu ƙarfi da kwanciyar hankali da wadata a yankin su kasance masu tasiri," in ji shi.