Daliban Turkiyya na gudanar da ayyukan alheri da gina kasa a Afirka. Hoto: AA

Kungiyoyin dalibai ne da dama da suka fito daga jami'o'i daban-daban na Turkiyya wadanda suke kan wata manufa nesa daga gidajensu.

Taken shirin nasu na "Mun Rufta Bakar Soyayya, Mun Tafi Gangami" ba shi kadai ne takensa ba, wata shaida ce ta tafiyar kawo sauyi daga wadannan daliban jamio'i, wadanda suke karkashin inuwar Kungiyar Matasan Kasa da Kasa, suna aiki a matsayin jakadun fata nagari, yayin da suke koyon yadda kyautatuwar zamantakewa take a aikace.

Babbar manufar shirin ita ce a samar da yanayin da Turkiyya za ta mu'amalanci Afirka. A wani bangare na wannan aiki na musayar al'adu, zababbun daliban jami'o'in sun isa ga yankunan kasashen Afirka daban-daban.

Manufarsu? Ita ce su shiga dukkan ayyukan ci gaban al'umma, suna bayar da gudunmawa wajen ingantuwar jama'arsu.

Nutso a cikin al'adun Afirka na fadada damarmaki tare da kawo yaba kyawun bambance-bambance.

Amma wannan aiki ya wuce batun karamci kawai, batu ne na nagarta a duniya yayin da suke samun kwarewar kasa da kasa a tsakanin masu gudanar da aikin.

A lokacin da daliban suke zuwa iyakokin Afirka, suna zama wakilan samar da canji, suna dauke da buruka da fata nagari na duniya baki daya, ba wai na kasashensu kawai ba.

Sun zama manufar dabbaka ayyuka na nagarta a duniya, suna nuna muhimmancin hadin kan mutane a lokacin da suka hadu da juna.

Ka dauki Huseyin Aslan a matsayin abun misali. Dalibin lissafi a Jami'ar istanbul Medeniyet, wanda yake daga cikin mambobin kungiyoyi hudu da suka tafi Tanzania.

Tafiyarsu ta faro ne da manufar yin kwaskwarma ga makarantar Nur Madrasa, wata makarantar Islamiyya da ke birnin Dar es Salaam na Tanzania.

A tsawon kwanaki biyar, wadannan matasa masu aikin sa kai sun sadaukar da kawunansu ga aikin farfado da wajen koyo da koyarwar dalibai 190, suna yin fenti ga ciki da wajen makarantar.

A yayin da ake shafa fentin karshe, sai suka gudanar da addu'o'i tare da daliban makarantar, suna keta iyakokin al'adu da na yaruka.

Dabbaka hadin kai da fahimtar juna ta hanyar musayar al'adu a Afirka.

Tasirin kwarewar da ya samu, kamar yadda Huseyin ya shaida wa TRT World, abu ne da zai yi wahala a bayyana shi da kalmomi. Domin fahimtar karsashin da ke tare da wannan aiki a wajen kasarka, sai ka je can kawai, in ji shi.

A Tanzania, inda Musulunci ya je yankin a karni na tara, masu aikin sa kan sun shaida irin farin cikin da ruwa mai tsafta yake kawo wa jama'ar kauyukan da ke nesa.

An samar da rijiyoyi masu ruwa mai tsafta da tallafin Turkiyya a lambunan makarantun kauyen Kibesa da ke Masaki, inda ake aike wa da sakon nuna muhimmancin ilimi. Rijiyoyin na taimaka wa wajen tabbatar da samun tsaftataccen ruwan sha d akawo sauyi a fannin ilimi.

Huseyin bai iya taimaka wa yadda ya so ba, amma ya samu gamsuwa da irin yalwa da wadatar da yake da ita a wayuwarsa.

Tanzania, kasar da Musulmai da Kiristoci suke rayuwa tare ba tare da wata matsala ba, ta zama wani babban misali na aminta da juna a karni na 21.

Waje ne da ba a yanke hukunci kan mutane ko a nuna musu wariya saboda addinin da suke bi.

Huseyin ya ji lallai wannan labari ne da ya kamata a bayar da shi, a karfafa fahimta da hadin kai ba tare da duba ga addinin mutum ba.

Tasiri mai dore wa na daliban Turkiyya a balaguron da suka yi zuwa Afirka.

Shirin "Mun Rufta Soyayya" na tunatarwa da cewa a lokacin da zukatan matasa d akuma tausayi suka hadu a waje guda, za su iya samar da sauyi mai kyau a yankunan da suke wajen nasu.

Wadannan dalibai da suke duke da ilimansu da jajircewa, na taimaka wa wajen sauya fasalin duniya tare da haskaka ta. Ta hanyar sadaukarwarsu, ba wanzuwar Turkiyya kadai suke fadada wa a Afirka ba, suna kuma inganta rayuwar mutanen da suke agazawa.

A bangaren Halil Ibrahim Aksen kuma, dalibin da ke nazarin Kimiyyar Siyasa da Alakar Kasa da Kasa a Jami'ar Ibn Haldun da ke Istanbul, ya samu tasa kwarewar da bayar da hidima a Uganda.

A yayin da ya tsinci kansa a tsakanin sabbin al'adu, ya gano muhimmancin aikin alheri komai kankantarsa. Ya ga da bayar da kayan wasa ke sanya farin ciki a zukatan yara kanana.

Hamza Erfidan kuma dalibin sadarwa ne da ke karatu a Jami'ar Galatasaray da ke Istanbul, ya tsinci kansa a Sanagal, wajen da fuskanta da gano sabbin al'adu ya zamar masa wani jigo.

Abun da ya fi ba shi mamaki shi ne irin tarbar da aka yi masa a Sanagal. Yanayi da wjen da Dakar da Thies suke ba ya fi karfin waje a taswira kawai, sun zama wani bangare na labarinsa.

Yadda jama'ar yankin suke a shirye wajen bayar da gudunmowa da aminta da su, ya zama abun da kwakwalwarsa ba za ta taba mantawa ba.

Tasiri mai dore wa na daliban Turkiyya a balaguron da suka yi zuwa Afirka.

"Game da kalubalen da ake samu kan bambancin al'adu, sauyin yanayi da sauran batutuwa, jama'ar Senegal sun nuna kyautayi da tarba mara misaltuwa, suna sauya kalubale ya zama damarmaki don habaka da cigaban mutane," in ji Erfidan yayin tattauna wa da TRT World.

Duk wata ganawa da haduwa da mutane na tuna wa Hamza kyawun da ke tattare da rungumar bambance-bambance, da kuma iyawar mutane wajen yin aiki tare don magance matsaloli.

Wannan ba wai abu ne na bayyana kwazon Senegal ba, batu na na bayyana yadda jama'a suke taimakon juna su samar da wani abu mai kyau daga bamance-bambancen da ke tsakaninsu.

Mai sana'ar zane da taswiri Rabia Sevinc kuma ta je Ghana. Ta fada wa TRT World cewa "Mun bar Turkiyya tare da mata matasa su bakwai, da manufar yin kwaskwarima ga azuzuwa biyu a a makarantar Darul Hijra ta Islamiyya da ke Accra, babban birnin Ghana, tare da samar musu da kayan aiki don taimaka wa dalibai wajen koyo da koyarwa.

Muna aikin wkaskwarimar sannan muna wasa da yara a makarantar. Suna kallon mu a koyaushe idan muna aikinmu. Abun farin ciki ne ganin yadda yaran suke murna a yayin da muke gyara musu makarantarsu."

Ta kara da cewa "Ghana kasa ce da ke da al'adu daban da wadanda na saba da su. Wannan ya sa na ke kallon kowa da komai cikin mamaki.

Ina haduwa da sabuwar al'ada, amma jama'ar na da son abota da kuma saurin saba wa da baki, ban ji ni a matsayin bakuwa ba.

Kyawun jama'a da yanayin kasar ya bayar da gudunmowa wajen hakan sosai. Korran tsirrai na Ghana sun ja hankalinmu sosai."

Masu aikin sa kai sun hadu a gargajiya da al'adun Afirka

Labaran wadannan matasa na bayyana karfin kawo sauyi a yayin musayar al'adu da tasiri mai dorewa wajen taba rayuwar masu bukata.

Ba wai iya taimakon kayayyaki da aka baiwa mutanen ba, har ma da batun gadoji da hadin kan da suka kafa.

Kowanne daga wadannan masu bayar da gudunmowa, a nasu bangaren, sun taimaka wajen sake kulla duniya mai haske da walwala.

TRT World