Za a dinga kada kuri'a daga karfe 9 na safe zuwa 9 na yammacin lokacin kasar a ranakun aiki da na karshen mako / Hoto: AA

'Yan Turkiyya mazauna kasashen waje ma suna da damar kada kuri'a a zabukan shugaban kasa da na majalisar dokoki daga kasashe 74 a wurare 177 daga ranar 27 zuwa 9 ga Mayu.

Mutane za su kada kuri'a a ofisoshin jakadanci 177 a kasashe 74 har zuwa ranar 9 ga watan Mayu daga karfe 9 na safe zuwa 9 na yammacin kasar a ranakun aiki da na karshen mako, kamar yadda Majalisar Koli ta Zaben Turkiyya ta fada.

A biranen da ake da kananan ofisoshin jakadancin Turkiyya kuwa, za a yi zaben daga karfe 9 zuwa 6 na yamma ne kawai.

Sannan kuma masu zabe za su iya kada kuri'a a kowane ofishin jakadanci ko cibiyoyin hukumar kwastam inda aka ajiye akwatunan zabe, ba tare da mutum ya nemi a ba shi lokaci ba gabanin hakan.

A yanayin da babu wanda ya samu fiye da kashi 50 na yawan kuri'u daga cikin 'yan takarar, za a sake kada kuri'a a zabe zagaye na biyu, da aka tsara yin sa ranar 28 ga Mayu, inda za a gudanar da shi a ofisoshin jakadanci daga tsakanin 20 zuwa 24 ga Mayun.

Za a yi zabe a wurare 26 a Jamus da kuma wurare tara-tara a Amurka da Faransa.

Kusan 'yan Turkiyya miliyan 6.5 ne ke zaune a wasu kasashen. Daga cikinsu kuma miliyan 3.28 ne suka cancanci kada kuri'a a zabukan da ke tafe na shugaban kasa da majalisar dokoki.

Adadin masu zabe daga kasashen waje dan kadan ne idan aka kwatanta da masu yin zabe daga cikin Turkiyya mai yawan miliyan 60.9.

Amma a yanayin da ake kusan kan-kan-kan tsakanin 'yan takarar, kuri'un mazauna kasashen wajen ba karamin tasiri zai iya yi ba, kamar dai yadda aka gani a zaben 2018 da ya sa Erdogan ya yi nasara.

Mafi yawan 'yan Turkiyya da ke waje na zaune ne a Yammacin Turai, inda ma'aikatan Turkiyya suka fara zama tun a shekarun 1960 a wani bangare na shirin sake gina yankin daga barnar Yakin Duniya II. Su ne suka gina al'ummar Musulmai mafi girma ta 'yan ci rani a Yammacin Turai.

'Yan Turkiyya da ke aiki a kasashen waje sun fara kada kuri'a ne a karon farko a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Agustan 2014 inda Erdogan ya yi nasara da kashi 62.2 cikin 100 na yawan kuri'un.

A tsarin doka, duk wani ma'aikaci dan Turkiyya a kasar waje da ya haura shekara 18 kuma sunansa yake kan rajistar ofishin jakadanci to zai iya yin zaben.

'Yan Turkiyya mazauna kasashen waje da ke kada kuri'a sun fi yawa a Jamus inda yawansu ya kai miliyan 1.4, daga nan sai Faransa da Netherlands da kuma Belgium.

TRT World