Aikin hanya na Pile-Yigitler da ake yi a Pile, wanda ake yinsa domin samun hanya ga Turkawa ‘yan Cyprus, aiki ne na jinkai, kamar yadda mataimakin shugaba kuma kakakin Jam’iyyar AK, Omer Celik ya bayyana.
Ya fadi haka ne bayan rashin jituwa da aka samu tsakanin ‘Yan sanda Arewacin Cyprus da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
An samu rashin jituwar ne da misalin 9:00 na safe (0600 Agogon GMT) a ranar Juma’a kan hanyar Pile-Yigitler, wadda ake ginawa da kuma fadadawa, kamar yadda Babbar Hukumar ‘Yan sanda da ke Jamhuriyar Turkiyya ta Arewacin Cyprus a wata sanarwa da ta fitar.
Jami’ai takwas aka raunata a yayin rikicin kan batun wurin ajiye ababen hawa a kan iyakar da ta raba arewaci da kudancin Cyprus wadda Majalisar Dinkin Duniya ke iko da ita, kamar yadda ‘yan sandan Arewacin Cyprus suka tabbatar.
"Dagangan" jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka faka motocinsu kan hanya inda suka toshe hanyar da ake aiki domin hana aikin hanya inda suka ki bin ka'idar tsaro da 'yan sanda suka saka.
“Matsayar da MDD ta dauka kan masu Aikin Wanzar da Zaman Lafiya na MDD a Cyprus kan batun aikin hanyar Pile-Yigitler ba mu amince da ita ba,” in ji Celik a sanarwarsa.
“Abin da dakarun wanzar da zaman lafiyar suka yi, wanda suka yi shi ne domin dadada wa Girkawa da ke Cyprus, kai tsaye ya zubar da mutuncinsu a Cyprus,” kamar yadda ya kara da cewa.
Hukumar gudanarwa ta Cyprus da Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah-wadai da aikin Pile-Yigitler wanda TRNC ta soma aiwatarwa a ranar Alhamis.
Mazauna Pile za su iya amfani da hanya mara nisa, inda ba sai sun kutsa ta sansanonin Birtaniya a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa Turkiyya ba sakamakon gini da gyaran hanyar Pile-Yigitler mai nisan kilomita 11.6.
Kilomita 7.5 ta farko ta hanyar za ta ratsa ne ta Yigitler ta biyu kuma za ta bi ta kauyen Pile.