Gwamnan Malatya Ersin Yazici ya ce "Ba mu samu labarin wani mummunan abu ba. Jami'anmu na ci gaba da aiki a yankin." /Hoto: AA Archive

Girgizar kasa mai karfin maki 5.2 ta afku a Lardin Malatya na gabashin Turkiyya, in ji hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar.

Hukumar Yaki da Annoba da Bayar da Agajin Gaggawa ta Turkiyya (AFAD) a ranar Alhamis din nan ta bayyana cewa girgizar ta afku a gundumar Battalgazi a karkashin kasa da zurfin kilomita 13,93 da misalin karfe 1604 agogon Turkiyya (1304GMT).

An ji motsin girgizar kasar a largunan da ke kewaye da lardin Malatya.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Gwamnan Malatya Ersin Yazici ya ce "Ba mu samu labarin wani mummunan abu ba. Jami'anmu na ci gaba da aiki a yankin."

Bayan afkuwar girgizar kasar, Ministan Harkokin Cikin Gidan Turkiyya Ali Yerlikaya ya ce ba a samu rahoton samun wata barna ba sakamakon ibtila'in, kuma an kai jami'an don bincike da gano ko akwai wata matsala da ka iya afkuwa.

Bayanai kan girgizar kasar

- Karfin maki 5.2 - Zurfin kilomita 13.93 - Babu rahoton wata ɓarna ko asarar rai - Tawagogin agaji na cikin shirin ko ta kwana

TRT World