Ma’aikatar Harkokin Waje ta Turkiyya ta sanar da cewa an sake zabar Turkiyya domin kasancewa mamba a Kungiyar Kasashe Masu Safara da Jiragen Ruwa (IMO).
A wata sanarwa da ma’aikatar ta saki, ta bayyana cewa an gudanar da zaben na IMO a ranar Juma’a a lokacin taron kungiyar na 33 da ake yi a birnin Landan.
Turkiyya ta kasance ‘yar kungiyar kuma aka sake zabarta domin ci gaba da kasancewa a matsayin mamba, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
“Turkiyya wadda aka zabeta a matsayin mamba a zaben da ake gudanarwa na kungiyar tun daga 1999, za ta ci gaba da bayar da gudunmawa mai yawa a aikin IMO, musamman duba da kwarewar da take da ita da gogewa ta fannin sufurin ruwa,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.
A yayin da yake karin bayani game da yadda aka gudanar da zaben, Ministan Sufuri da Ababen More Rayuwa na Turkiyya Abdulkadir Uraloglu ya bayyana cewa an zabi Turkiyya a matsayin mamba a kungiyar IMO “a karo na 13 a jere inda ta samu kuri’u mafi yawa a tarihi da goyon bayan kasashe 143.”
“Baya ga goyon bayan da muka samu a zaben akwai manufofi masu nasara da kuma matakai na hakika da muka dauka daidai da dokokin kasa da kasa a fannin teku, da kuma yadda muke aiki tukuri a ayyukan IMO.”