Recep Tayyip Erdogan: An gano Lafarge na daya daga kamfanunnukan dake daukar nauyin ta’addanci

Kamfanin samar da siminti na Faransa ya zama daya daga cikin kamfanunnukan dake daukar nauyin ta’addanci, in ji Shugaban Kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan.

Erdogan ya bayyanawa taron Ministocin Yada Labarai na Kasashen Hadin Kan Musulmi karo na 12 da aka gudanar a Istanbul cewa, “A lokacin da na bayyana cewa babban kamfanin samar da siminti na Fraransa Lafarge, ya taimakawa ‘yan ta’adda a arewacin Siriya, gwamnatin Faransa ba ta fahimci hakan ba. Na fadawa Shugaban faransa Emmanuel Macron wannan. Yanzu a Majalisar Dokokin Faransa, suna tambayar Macron ba’asi game da Lafarge,”.

Erdogan ya kara da cewa, “A yanzu haka, Lafarge ya zama daya daga cikin batutuwa mafiya muhimmanci da ake tattaunawa a Faransa. An gano kuru-kuru yadda Lafarge ya zama daya daga cikin manyan kamfanunnuka masu goyon bayan ta’adddanci.”

Babbar tara

A ranar Talata kotun Amurka ta yankewa Lafarge tarar dala miliyan 778 saboda taimakawa kungiyoyin ‘yan ta’adda da dama a arewacin Siriya da suka hada da Daesh a tsakanin 2013-2014.

Erdogan ya ce, duk da Turkiye ce kadai kasar dake yaki da ‘yan ta’addar Daesh a fagen daga, amma kuma ana yi mata “mummunan zato”.

Ya kara da cewa “A yau, daya daga cikin hukuncin kotu ya bayyana yadda wadanda jiya suke bata mana suna suka yi kasuwanci da Daesh, suka aikawa ‘yan ta’adda miliyoyin kudaden Yuro a wannan lokacin,”.

AA