Masu gabatar da kara a Turkiyya sun tasa keyar wasu ‘yan Isra’ila biyu zuwa gidan yari bayan an tsare su bisa zargin leken asiri da sunan kasuwanci.
A wani samame da hukumar binciken ayyukan ta'addanci da wasu manyan laifufuka ta ofishin babban mai shigar da kara a Istanbul ta gudanar, an gano cewa mutanen biyu da ke aiki a madadin kamfanin leken asirin Isra'ila, sun zo babban birnin kasuwancin Turkiyya ne don shirya ganawa da Omar A, wani Bafalasdine mai kera manhajoji.
A cewar ofishin mai shigar da karar, a baya wani kamfani mai alaka da jami’an leken asirin Isra’ila ya tattara bayanai kan Omar A. inda ya aika masa da tayin aiki da wadanda ake zargin suka shaida masa cewa suna son tattaunawa a kai.
Sun kuma tura kudi zuwa asusun Omar A. kan wani aikin gwaji da ya shirya musu.
An taba tsare daya daga cikin wadanda ake zargin a filin jirgin saman Istanbul a ranar 7 ga watan Oktoba, bisa zarginsa da laifin leken asiri kan ''ayyukan soji da na siyasa,'' sakamakon bayanan da aka samu na cewa yana da alaka da jami'an leken asirin Isra'ila.
An kuma tsare daya mutumin da ake zargi da laifin leken asirin Turkiyya a madadin Tel Aviv.