An haife ta a Turkiye a shekarar 1998. Sojojin Isra’ila sun kashe ta tana da shekara 26 kacal. / Hoto: AP

An binne Aysenur Ezgi Eygi, Baturkiya kuma Ba’amurikiya ‘yar gwagwarmaya wadda sojojin Isra’ila suka kashe a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a makon da ya gabata. Ana gudanar da jana’izar ne a garinsu da ke Didim a Turkiyya.

“Aysenur Ezgi Eygi, kamar duka sauran shahidanmu, tana nan a raye a gare mu,” in ji Kakakin Majalisar Turkiyya Numan Kurtulmus a jawabin da ya gabatar a Didi, a lokacin da ya yi wa iyalan Aysenur ta’aziyya. “Ruhinta na ba mu ƙwarin gwiwa,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Eygi mai shekaru 26, ta kasance a Beita, Nablus, cikin lumana, tana nuna rashin amincewa da matsugunan ‘yan kama wuri zauna na Isra'ila, lokacin da aka sojojin Isra'ila suka harbe ta a kai da bindiga, lamarin da ya sa ta mutu.

Kurtulmus ya sha alwashin cewa,Turkiye za ta kama Isra’ila da alhakin kisan da ta yi, kuma Tel Aviv za ta amsa laifin da ta aikata a kotunan duniya.

Iyalan Eygi sun samu rakiyar mataimakin shugaban Turkiyya Cevdet Yilmaz da Ministar Harkokin Iyali da Rayuwa Mahinur Ozdemir Goktas da Ministan Shari’a Yilmaz Tunc da Ministan Harkokin Cikin Gida Ali Yerlikaya da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan.

An haife ta a Turkiye a shekarar 1998. Sojojin Isra’ila sun kashe ta tana da shekara 26 kacal.

A ranar Juma'a ne aka mayar da gawar Eygi zuwa kasar Turkiyya domin gudanar da bincike na likitoci a kan gawar da binne ta.

Sakamakon farko na binciken gawar da aka yi, wanda aka gudanar a Cibiyar Magunguna ta Izmir, ya bayyana raunin da aka samu a kai sakamakon harbin da aka yi a ƙasan kunne.

An rubuta dalilin mutuwar a matsayin "karyewar kwanyar, zubar jini na kwakwalwa, da lalacewar nama na kwakwalwa." An tabbatar da cewa akwai raunin shiga harsashi a kai, amma babu raunin fitar harsashi.

An ‘yan ƙananan ƙarafa a cikin kanta waɗanda aka ɗauka domin gudanar da bincike. An gudanar da gwajin farko kan gawara a makon da ya gabata a Cibiyar Nazarin Magunguna ta Jami'ar An-Najah ta kasa a Nablus.

Sakamakon ya tabbatar da cewa harbin bindiga da maharbi ya yi a kai ya yi sanadiyar mutuwar Eygi.

TRT World