A wata gagarumar nasara, Turkiyya ta kammala aikin samar da iskar gas dinta da ke yankin Sakarya cikin kasa da shekara uku, ana sa ran iskar gas din za ta fara kwarara daga rijiyoyin da ke gabar tekun Bahar Aswad a wannan mako.
Masu suka sun nuna shakku game da dagewar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi cewa za a yi aikin a kan lokaci, a sanarwarsa ta watan Agustan shekarar 2020 lokacin da ya ayyana cewa za a kammala aikin a shekarar 2023.
"Hakika, wannan babbar nasara ce, ko da kuwa an yi sauri, a bisa ka’ida a kan iya kwashe shekara hudu kafin a kammala aiki irin wannan na kan teku, za mu iya cewa sashen man fetur na Turkiyya ya kamala aikin cikin sauri," in ji Shugaban Kamfanin makamashi na GazDay da ke Santabul Mehmet Dogan.
Kamfanin mai na Turkiyya TPAO ya samar da rijiyoyi da dama a yankin Sakarya da ke da tazarar kilomita 175 daga birnin Eregli na gabar teku, tare da hadin gwiwar manyan kamfanonin aikin injiya biyu na Subsea7 da Schlumberger.
Ga wasu muhimman bayanai game da aikin na biliyoyin daloli.
Ta ya aka kammala shi da sauri?
Sakarya wuri ne mai zurfin gaske, hakan na nufin dole sai an yi haka ta dubban mitoci zuwa kasa da gabar teku don isa ga ma'adanar iskar gas.
Inganta hanyoyin mai a kan teku abu ne mai daukar lokaci saboda ana bukatar kwararrun injiniyoyi da amincewar tsare-tsare masu yawa.
Misali, iskar gas daga Sakarya za ta isa zuwa kasa ta bututun karkashin ruwa mai tsawon kilomita 170 sannan kuma ta wasu hanyoyin.
Baki daya dai, manyan kamfanonin mai kamar ExxonMobil da Royal Dutch Shell da TotalEnergies na Faransa ne kawai ke da arzikin iya shiga karkashin teku don neman mai.
Bayan da wasu kasashe da dama suka yi watsi da Turkiyya, sai Ankara ta yanke shawarar bin tata hanyar wajen mallakar jiragen hako mai a cikin ruwa, ciki har da jirgin hako mai na ruwa na karni na shida Fatih, a wani yunkuri na neman albarkatun mai da iskar gas a cikin zurfin teku.
Kuma kasancewar TPAO a karshe ya zama mamallakin yankin na Sakarya 100 bisa 100, ya bayyana yadda ci gaban aikin ya kasance cikin gaggawa.
Masu masana'antu sun ce kamfanonin mai na kan teku masu zaman kansu kan yi fama da tsaiko na cike-ciken takardu da bin ka'idoji da yarjejeniyar saye.
Don haka a matsayinsa na kamfanin gwamnati, TPAO ya sami damar rage yawan lokacin da ake bi wajen kulla yarjejeniyar cinikayya na farashi da doguwar yarjejeniyar saye da sayarwa.
Me ya sa Turkiyya ta yanke shawarar yin aikin da kanta?
Shekaru da dama da suka gabata, Turkiyya ta dogara ne kan makamashin da ake shigowa da su daga kasashen waje domin mahukunta da kamfanoni masu zaman kansu a kasar duk sun yi amanna cewa ilimin karkashin kasa na kasar ba shi da karfin taimakawa wajen samar da ma'adanar ruwa.
Sai dai, a binciken da aka yi nasarar gudanarwa a jere da kasashen yankin kamar Isra'ila tare da matakin cire Turkiyya daga fagen makamashin Gabashin Bahar Rum ya ingiza Ankara ta hanzarta kokarinta a fannin samar da makamashinta.
A 2017, a wani sabon tsari, Turkiyya ta sayi jiragen ruwa masu hako ma’adanai daga karkashin teku don fara bincike a cikin yankunan ruwanta, kuma Ankara ta sanya jiragen ruwa uku wato Fatih da Yavuz da Kanuni don fara neman albarkatun man fetur a Gabashin Bahar Rum da Bahar Aswad.
A yanayi irin na yankin Sakarya, a baya TPAO ya yi aiki tare da hadin gwiwar kamfanoni irin su Chevron da Petrobras, sai ya fara neman albarkatun mai da iskar gas a Gabashin Bahar Rum da Bahar Aswad da kansa, saboda yadda kamfanoni suka nuna sha’awarsu ta daina da aiki tare.
Alal misali, a shekarar 2004, kamfanin man fetur na Birtaniya ya gano iskar gas a cikin wata rijiya mai suna Ayazli-1 da ke cikin Bahar Aswad, amma ya yi watsi da ci gaban binciken ya kuma bai wa TPAO izinin ci gaba da aikin.
Ƙarfin makamashin Bahar Asawad da Bahar Rum inda kasar Masar ta sami babban filin Zohr Gas a 2015, ya kasance ba a wani amfani da shi, a cewar masana.
Adadin iskar Gas nawa za ta samar?
Za a kammala aikin Sakarya cikin rukuni daban-daban, ana sa ran samun iskar gas har adadin kubik mita tan miliyan 10 a rana, adadin da ya kusan kai kashi 10 na wanda ake amfani da shi a lokacin zafi.
"Kazalika kuma kashi hudu zuwa biyar na yawan iskar gas da ake amfani da ita lokacin sanyi domin mutane na kunna na’urar dumama daki," in ji Dogan.
“A rukuni na biyu wanda za a kamala a tsakanin shekarar 2027 zuwa 28, a duk rana ana sa ran samun kubik mita tan sama da miliyan 40, akwai yiwuwar hakan ya iya kai wa kashi 25 na yawan iskar gas da Turkiyya ke amfani da ita.’’
A bara, Turkiyya ta yi amfani da adadin iskar gas kubik mita biliyan 54 na gas, wanda kusan gaba daya an shigo da shi ne daga kasashen Azerbaijan da Rasha da sauran wasu kasashe.
Dogan ya ce gaba daya adadin da ake amfani da shi ya karu a cikin shekarun nan tare da sabbin gine-gine da fadada hanyoyin tattalin arziki.
Amma a bara yawan iskar gas da aka yi amfani da shi ya yi kasa da kubic mita tan miliyan 60, adadin da aka tattaro na 2021, saboda karfin hadin makamashin da aka rarraba a 2022 ya biyo bayan yawan ruwa da aka samu.
Mene ne tasirinsa ga tattalin arziki?
Idan aka auna farashin iskar gas a ma’auni, iskar gas daga Sakarya za ta samar riba ga tattalin arziki da kusan dala miliyan biyar, a cewar Dogan.
Ko da yake, adadin na iya karuwa sosai idan aka samu hauhawar farashi na makamashi.
Yakin da ake ci gaba da yi a Ukraine da gazawar bankunan Amurka ya durkusar da hasashen da ake yi na tattalin arzikin duniya tare da rage farashin man fetur da iskar gas.
“Idan farashin iskar gas ya yi tashin gwauron zabo kamar na bara, ba shakka ribar za ta yi gwabi,’’ in ji Dogan.
Farashin zai taka muhimmin rawa wajen tabbatar da tasirin iskar gas na Sakarya, saboda Turkiyya ta kashe dala biliyan 80 wajen shigo da makamashi daga kasashen waje a bara. Lissafin da ya lalata farashin canjin kudin kasar a idon duniya.
Turkiyya a matsayin cibiyar kasuwanci
A watan Oktoban bara ne, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar cewa za a mayar da Turkiyya wata cibiyar makamashi da ke hada kasuwannin masu amfani da cibiyoyin samar da makamashi.
Hakan ya sanya Turkiyya a matsayin kasar da ke kan gaba wacce tuni ta riga ta zama hanyar jigilar manyan bututun iskar gas.
Dogan ya ce idan kasa ta zama cibiyar kasuwanci, dole ne ta kasance tana samar da iskar gas na cikin gida - wani abu da yankin Sakarya ke samarwa.
"Ina da tabbaci a kan wannan aiki, Turkiyya za ta karfafa zamanta a matsayin wata hanya ta samar da kayayyaki zuwa ga kasashen Turai da dai sauransu."