Daga mummunar girgizar kasar da ta faru a ranar 6 ga Fabrairu da ta yi ajalin sama da mutane dubu hamasin, zuwa nasarar Shugaba Recep Tayyip Erdogan a zabe karkashin taken "Shekaru Dari na Turkiyya", da bukin cika shekaru 100 da kafa Jumhuriyar Turkiyya, kasar ta zama dunkulalliya a yayin da ake shirin shiga 2024, za ta tafi da darussan juriya da ci gaba zuwa ga sabuwar shekarar.
Tare da nasorori a bangaren wasanni da fasahar kere-kere, Turkiyya ta hau babban matsayin ci gaba a 2023.
Ci gaba a rundunar sojin ruwa da ayyukansu, inda aka kammala ƙera jirgin ruwan yaki na Tyurkiyya mai daukar jiragen sama na yaki mara matuki irin sa na farko a duniya, ya daga martabar Turkiyya a tsakanin sojojin kasashe.
Haka ma a 2023, kaddamar da motar Togg kirar Turkiyya da ke amfani da lantarki, ta bude sabon shafin kera motoci a kasar.
‘Ibtila'in kasar’
Munanan girgizar kasa guda biyu sun afku a Turkiyya, awanni tara a tsakani, a ranar 6 ga Fabrairu, ta janyo asarar rayuka da dama a larduna 11 da ke kudancin kasar.
A cibiyar girgizar kasar, Pazarcik da Elbistan da ke lardin Kahramanmaras, girgiza mai karfin awo 7.7 da 7.6 sun afku a karkashin kasa da zurfin kilomita bakwai, inda suka dauki sama da dakika 30 suna motsa kasa.
An samu kananan girgizar kasa sama da 6,000 a cikin makonni biyu bayan na farkon da suka afku.
An bayyana girgizar kasar a matsayin "Ibtila'in Karni" saboda asarar rayuka da yawan jama'ar da suka mutu.
Girgizar kasar ta illata lardunan Adana da Adiyaman da Diyarbakir da Elazig da Hatay da Gaziantep da Kahramanmaras da Kilis da Malatya da Osmaniye da Sanliurfa.
Girgizar ta yi ajalin sama da mutum 50,000 inda kusan 115,000 suka samu raunuka. Girgizar ta shafi sama da mutum miliyan 13.5 a Turkiyya, inda ta tilastawa miliyan 3.5 sauya matsuguni zuwa wani yanki ko gari na daban.
A saniyoyin farko na girgizar kasar, dubban mutane sun rasa matsugunansu, wasu sun kasance a karkashin buraguzan gine-ginen da suka rushe.
'Yan kasar Turkiyya da ma gwamnati, tare da sauran jama'ar duniya, sun kawo agaji ga wadanda girgizar kasar ta rutsa da su.
Dubunnai sun bayar da gudunmowa sosai wajen bincike da kubutar da mutane, wasu kuma suka bayar da gudunmawar kudade da kayayyaki.
Gwamnati, wadda ke da alhakin kula da gangami da bincikowa da kubutar da mutane da sake gina farfadowa da gina yankin, ta yi ayyukan ba gajiyawa tare da 'yan sa kai don samar da waraka ga kasar.
TCG Anadolu - Babbar nasarar fasahar kere-keren kayan sufurin teku a Turkiyya
A watan Afrilu, Turkiyya ta marabci karbar TCG Anadolu, jirgin yakinta na ruwa mafi girma, kuma jirgin ruwa mai daukar jiragen sama na farko mara matuki a duniya.
Wannan kari mai muhimmanci da aka samu ba karfin sojin ruwan Turkiyya kadai ya karfafa ba, har ma da saka kasar a matsayin kasashe 'yan kadan na duniya da suka samar jirgin ruwan daukar jiragen sama da kansu.
An bai wa jirgin ruwan sunan TCG Anadolu. Babban jirgin ruwan, na iya daukar jirage masu saukar ungulu da jiragen yaki marasa matuki da motocin yaki da kananan jiragen yaki da kuma ma'aikata.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar a Istanbul, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada matsayin jirgin ruwan, ya bayyana shi a matsayin jirgin ruwan yaki na farko a duniya inda jiragen yaki marasa matuka da na yaki masu saukar ungulu mafiya girma suke iya tashi da sauka a kansa.
"Da yake bayyana kyawu da ingancin jirgin, Erdogan ya ce, "Jirgin TCG Anadolu... shi ne na farko a duniya da jiragen yaki marasa matuka manya za su iya tashi da sauka a kai."
Jiragen yaki marasa matuka na Turkiyya Bayraktar TB3 da na Kizilelma, tare da jirgin kai hari mai suna Hurjet, na da ikon tashi da sauka daga a kan jirgin ruwan.
Baya ga karfin ayyukansa, TCG Anadolu na da tsarin harba makamai da kula da yaƙi da yaƙi da manyan makaman lantarki da fasahar bincike da infrare da bincike da hangen nesa da tsarin tsaro na torpedo da na'urorin radar, duk wadanda aka samar a cikin gida Turkiyya.
Jirgin TCG Anadolu na da tsayin mita 231 da fadin mita 32, kuma nauyinsa ya kai tan 27,000.
Cigaba a Fannin Sufuri: Motar Togg Mai Aiki da Lantarki
A watan na Afrilu dai, Turkiyya ta sake shiga wani sabon shafi na ciba a fannin ƙera motoci, tare da motar farko da kasar ta samar mai aiki da lantarki ta Togg.
A watanni ukun farko na 2023 ta fara fitar da kirar SUV ta motar, inda kamfanin yake da manufar nan da 2030 za ta fitar da nau'ikan motocin biyar; SUV, sedan, C-hatchback, B-SUV, da B-MPV.
Batiran motar da ake samarwa da sinadarin lithium, na iya samun kaso 80 na caji a cikin mintuna 30, kuma za a iya tafiyar kilomita 500 da cajin.
A watan Disamban 2019 aka kaddamar da fara kera Togg, kuma nan da 2030 za a samar da guda miliyan daya da suka hada nau'ika biyar din.
Motar Togg mai aiki da lantarki na bayyana yadda Turkiyya ta mayar da hankali ga ci gaban kimiyya da fasaha, tana kuma zama wata babbar alamar kasar da ma makomarta.
A jawabin da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi na 'Shekaru Dari na Turkiyya' ya bayyana rawar da wannan aiki ke da shi wajen makomar fasahar ƙere-ƙere a kasar inda yake cewa, "Ba ma gogayya da fasahar jiya ko ta yau.
"Muna tunkarar makomar fasaha ne, inda muke samar da mota ta farko da aka samar a Turkiyya mai aiki da lantarki. Tare da wannan kokari, samar da batira da tashoshin caji, muna shiryawa da kokarin kyautata makomar kasarmu."
Nasara: Erdogan ya samu kaso 52.18 a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa
A babbar nasarar da ya yi, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya lashe zaben watan Mayu da kaso 52.18 na kuri'un da aka jefa a zagaye na biyu na zaben, inda abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu kuma ya samu kaso 47.82.
Zaben ya shaida fitar masu kada kuri'a da kaso 84, inda sama da mutum miliyan 54 suka jefa kuri'a a zaben.
Da yake jawabi ga magoya baya da ke yin murnar lashe zabe a Istanbul, Erdogan ya ce "Mun fada za mu yi nasara ta hanyar da babu wanda zai yi asara. Turkiyya ce kadai ta yi nasara a yau.
"Ba tare da lahanta dimokuradiyya, cigaba da manufofinmu ba, yanzu mun bude kofar shiga Shekaru Dari na Turkiyya, amma tare muka bude babbar kofar."
Da yake bayyana shirin kasar na hadin kai da cigaba, Erdogan ya bayyana bukatar da ake da ita ta aiki ba gajiyawa don amfanin jama'ar Turkiyya.
Gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen ganin an magance illolin da girgizar kasar 6 ga Fabrairu ta janyo tare da sake gina garuruwan da suka rushe.
Bayan kammala zagayen farko na zaben ba tare da dan takarar da ya yi nasara r samun kaso 50 na kuri'un da aka jefa ba, Shugaba Erdogan ya samu kashi 49.51. Kemal Kilicdaroglu na jam'iyyar CHP kuma ya samu kaso 44.88.
Nasarar Volleyball: Turkiyya ta yi nasara sau biyu a 2023
Kungiyar kwallon volleyball ta mata ta Turkiyya masu sunan "Sarauniyoyin Raga" sun samu nasara mai tarihin gaske a 2023, inda suka lashe gasar CEV ta Turai da gazar Kasa da Kasa ta FIVB 2023.
Tare da karfin gwiwa da dabaru, zakarun na kwallon volleyball, zakarun na Turkiyya sun samu nasara, inda suka zana sunayensu a kundin tarihi, tare da kawo wa kasar abun alfahari da daukaka.
A watan Yuli, kungiyar kwallon volleyball ta mata ta ta lashe gasar 2023 FIVB, inda ta doke twakwararta ta China da ci 3 da 1 a wasan karshe.
Sarauniyoyin Raga da Daniele Santarelli ke baiwa horo, sun nuna karfi da kwarewarsu a Arlington, Texas inda suka lashe wasanni daban-daban da maki 25-22, 22-25, 25-19, da 25-16
Wannan babbar nasara ta tarihi ta kai Turkiyya matsayin lashe gasar FIVB 2023 a karon farko.
Nasarar ba wai daukaka ta baiwa Turkiyya a fannin wasanni kawai ba, har ma da karfafa kungiyar a fagen wasannin volleyball a duniya.
Kungiyar kwallon volleyball ta Turkiyya sun samu nasararsu ta biyu a 2023 watanni biyu bayan nasarar farko inda suka lashe gasar Kwallon Volleyball ta Turai CEV.
Kyaftin Eda Erdem Dundar, ta bayyana farin cikin kungiyar, ta kuma bayyana muhimmancin wannan nasara da cewa, "A yayin bikin cikar mu shekaru 100 da zama Jumhuriya, mun lashe Gasar Kasa da Kasa ta farko, sannan muka lashe gasar Turai. Mun kafa tarihin da ba zai gogu ba. Ina farin ciki. Ina alfahari!"
Bikin CIka Shekara 100: Ranar Jumhuriya ta Turkiyya
A wani yanayi na tarihi da ban sha'awa, Turkiyya ta yi bikin Ranar Dimokuradiyya a ranar 29 ga Oktoba 2023.
Mustafa Kemal Ataturk ne ya kafa Jumhuriyar Turkiyya, wannan lamari na tarihi na bayyana irin ruhin juriya da kasar ke da shi wand ake ci gaba da wanzar da ita
A fadin Turkiyya, an gudanar da bukukuwa, ana nuna cigaban da kasar ta samu a fannin kera kayan tsaro ta hanyar baje kayayyaki cikin nau'ika masu jan hankali.
Bikin cika karni guda na bayyana kyakkyawar tafiyar Turkiyya ta shekaru 100 - ci gaban kimiyya da fasahar kere-kere da hadin kai, waɗanda suka bayar da damar gina makoma mai kyau.
A Istanbul, jiragen yaki 100 ne suka yi rakiya ga TCG Anadolu don nuna murna da farin cikin cikar Turkiyya shekara 100 da zama Jumhuriya.