Ɗan wasan Manchester United Joshua Zirkzee yayin da yake murnar cin ƙwallonsu ta farko tare da Marcus Rashford./Hoto: REUTERS

Sabon ɗan wasan Manchester United Joshua Zirkzee ya ceto ƙungiyar daga hannun Fulham bayan ya ci ƙwallo a wasan da suka tashi da ci 1-0 a karawarsu ta farko ta gasar Firimiya ta bana.

Ɗan wasan ɗan ƙasar Netherlands ya zura ƙwallon ce a minti na 87 lokacin da Alejandro Garnacho ya miƙa masa ƙwallon a fafatawar da suka yi a filin wasa na Old Trafford ranar Juma'a da maraice.

Magoya bayan ƙungiyar sun kasance cikin murna gabanin soma wasansu, ganin cewa sun ƙaddamar da sabbin 'yan wasa huɗu.

Sai dai kamar yadda ya faru a kakar wasan da ta gabata, a karawarsu ta farko ta ranar Juma'a United ta yi ta ƙoƙarin danne abokan hamayyarsu, inda kyaftin ɗin ƙungiyar Bruno Fernandes ya zo dab da cim ma burinsu.

Sai dai hakan ba ta samu ba har sai lokacin da aka sanya Zirkzee a cikin wasan inda ya ceto United daga hannun Fulham.

TRT Afrika da abokan hulda