Za a yi gwanjon kyautar da marigayi Diego Maradona ya samu ta Golden Ball a shekarar 1986, wacce ta yi ɓatan dabo tsawon shekaru masu yawa.
An bai wa Maradona kyautar ne a birnin Paris saboda bajintar da ya nuna lokacin Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 1986 a kasar Mexico, wanda kasarsa ta Argentina ta lashe.
A shekarar ne Maradona ya jefa kwallo ragar Ingila da hannu, wacce ta shahara da kwallon ‘Hand of God’, sannan a wasan ne kuma ya kara jefa wata kwallon bayan ya gama yanke ‘yan baya ya yanke gola, abin da ya sa FIFA ta ce wannan kwallo ita ce kwallo ‘mafi fice’ a tarihi.
Sai dai jim kadan bayan bai wa Maradona kyautar ne sai ta yi batan dabo.Wajen gwanjon kaya na Aguttes ya ce an gano kyautar ne ta Maradona hade da wasu kayayyaki da aka yi gwanjonsu a shekarar 2016 a birnin Paris.
Ana sa ran za a sayar da kyautar a kan miliyoyin daloli a ranar 6 ga watan gobe a kasar Faransa.
Zargin sayar da kyautar
Wasu sun yi zargin cewa marigayin ne ya sayar da ita don ya biya bashin da ake binsa a lokacin.
Akwai kuma masu cewa Maradona ya ajiye kyautar ne a wani banki kuma wasu ’yan fashi suka je suka sace ta lokacin da suka yi fashi a bankin a shekarar 1989, yayin da dan wasan yake wani kulob a kasar Italiya.
Wajen gwanjon kaya na Aguttes ya ce an gano kyautar ne hade wasu kayayyaki da aka yi gwanjonsu a shekarar 2016 a birnin Paris.
To amma ba wannan ne lokacin farko da aka taba sace wata babbar kyauta ko kofi a fagen kwallo kafa ba.
Hatta shi kansa kofin duniya din an taba sace shi a shekarar 1966 a birnin London, gabanin fara Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar, wanda Ingila ta karɓi bakunci a shekarar.
Sai dai an gano kofin daga bisani da taimakon wani kare bayan mako daya.
Shekara 17 bayan haka, an sake sace kofin a karo na biyu, sai dai wannan karon a kasar Brazil ne a shekarar 1983, inda wasu mutane suka yi awon gaba da kofin lokacin da aka ajiye shi a cikin gilashi a hedkwatar hukumar kwallon kafa ta kasar a birnin Rio de Janeiro.
Kuma yau fiye da shekara 40 kenan da sace kofin, amma ba a iya nasarar gano shi ba. Hakazalika an taba sace Kofin Gasar Kasashen Afirka (AFCON) a birnin Cairo a hedkwatar Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Masar a shekarar 2020.
Mataimakin Sakatare na Kungiyar Marubuta Labarin wasanni reshen Jihar Kano Muzammil Dalha Yola ya ce bacewar irin wadannan kayayyaki yana da matukar mamaki.
Sannan masanin ya dora laifin kan sakacin mahukunta da masu harkokin kwallon kafa wadanda alhakin kare kayayyakin ya rataya a wuyansu.