Rahotanni na cewa za a yi gyara kan dokar da ta hana koci yin katsalandan ta hanyar taɓa ƙwallo yayin da take filin wasa. Hakan na zuwa ne bayan da aka bai wa kocin Arsenal Mikel Arteta yalon kati maimakon jan kati bayan ya taɓa ƙwallo.
Abin ya faru ne a wasan gasar Zakarun Turai da aka buga tsakanin Arsenal da Inter a 6 ga Nuwamban jiya, wanda aka doke Arsenal da ci 1-0. Arteta ya samu yalon kati bayan da ya ɗauki ƙwallo gabanin ta fita daga fili.
Abin da Arteta ya yi ya hana Matteo Darmian yin jifa, inda doka ta ce ya kamata a bai wa Arteta katin sallama daga fili.
An ruwaito shafin ESPN na cewa hukumar International Football Association Board (IFAB) mai lura da ƙa'idojin ƙwallo ta ba da shawarar sauya wannan dokar.
Tunanin da ake shi ne ba da katin gargaɗi ya wadatar kuma shi ya fi dacewa, matuƙar manufar koci ita ce ya taimaka wasa ya ci gaba cikin sauri.
Sauya doka biyu
Rahoton ya ƙara da cewa sauya dokar, wanda zai fara aiki a bazarar 2025, wajibi ya samu amincewar babban taron shekara na IFAB wanda za a yi a 1 ga Maris.
Ba da shawarar sauyin ta zo ne bayan wata doguwar tattaunawa a babban taron shekara da ya gudana ranar Litinin.
A shekaran nan, an sallami kocin West Brom, Carlos Corberan da kocin Kilmarnock, Derek McInnes daga filin wasa, saboda aikata irin wannan laifi. Shi kuwa Arteta bai samu wannan hukuncin daga alƙalin wasa Istvan Kovacs ba.
Bayan taron na Maris ya gudana, za a samu ƙarin bayanai kan takamaiman lokacin da wannan sauyi zai fara aiki.
Sannan rahotannin sun kuma yi nuni da cewa akwai yiwuwar a sauya dokar da ta tanadi abin da zai faru idan ƙwallo ta fita bayan ta bugi alƙalin wasa.