A Jum'ar nan ne 16 ga Agusta za a fara gasar Firimiya ta Ingila, wadda ta saba ɗaukar hankalin masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.
Manchester United za ta kara da Fulham a filin wasa na Old Trafford, wanda shi ne wasan farko na kakar wasa ta 2024/2025, inda za a buga wasanni 380 cikin zagaye sama da 38.
Shafin Goal.com ya ruwaito cewa kocin Manchester United, Erik ten Hag ya bayyana damuwarsa kan shirin tawagarsa gabanin wasan nasu na farko.
Ƙungiyar ta samo sabbin 'yan wasa irinsu Matthijs de Ligt da Noussair Mazraoui, waɗanda a Alhamis da ta wuce suka zo.
William ya bar Fulham
Ɗan wasan Fulham ɗan asalin Brazil mai shekara 36, Willian zai bar Fulham bayan shekara biyu a kulob ɗin, a cewar ɗan wasan ranar Juma'a.
A bara ɗan wasan wanda ya buga wa Arsenal da Chelsea a baya, ya sanya hannu kan kwantiragin ƙarin shekara guda a Fulham, wadda yanzu ta ƙare. Rahotanni sun ce yana shirin tafiya Saudiyya.
A Gasar Firimiya, Willian ya buga wa Fulham wasa 58 a matsayin ɗan tsakiya, inda ya ci ƙwallaye tara.
Wasan Man City da Chelsea
A ɓangaren Manchester City, gasar ta bana za ta fara ne a karawarsu da Chelsea ranar Lahadi.
Koci Pep Guardiola ya sanar da cewa za a yi wa ɗan wasan City, Oscar Bobb tiyata a Juma'ar bayan da ya karya ƙafarsa a wajen atisaye. Ana sa ran zai bar buga wasa tsawon wata uku zuwa huɗu.