Za a yi wasa tsakanin Galatasaray da Manchester United a Istanbul. / Hoto: AA

Manchester United da Galatasaray za su fafata a birnin Santambul a rukunin A a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

Manchester United za ta kara a wannan wasan ne ba tare da wasu shahararrun ‘yan wasanta ba irin su Mason Mount da Casemiro da Christian Eriksen da Lisandro Martinez wadanda suke fama da rauni sai kuma Marcus Rashford wanda aka dakatar da shi.

A watan Oktoba, Galatasaray ta ci Manchester United 3-2 a wasan da aka buga a Old Trafford. Tauraron dan wasan nan Mauro Icardi ne ya ci kwallo ana daf da tashi inda ya sa Galatasaray ta samu nasara a Ingila.

A wannan wasan, Icardi da Wilfried Zaha za su kasance ‘yan wasa wadanda suke barazana ga Manchester United wurin cin kwallo.

Sai dai dan wasan nan na Colombia Davinson Sanchez ba zai buga wa Galatasaray din ba sakamakon raunin da aka gano yana da shi.

Za a soma wasan na Galatasaray da Manchester United da misalin karfe 17:45 a filin wasa na RAMS Park da ke Istanbul a ranar Laraba.

Bayern Munich ce ke sama a rukunin A bayan ta samu maki 12 a wasanni hudu. Copenhagen da Galatasaray duka sun samu maki hudu inda suke na hudu sai Manchester United ke biye a baya da maki uku a wasanni tsakanin rukunai hudu.

TRT Afrika da abokan hulda