Wa zai yi nasara wasan?:Hoto/Getty Images

A duk lokacin da yaran Pep Guardiola da yaran Jurgen Klopp suka hadu a gasar Firimiya, wasansu ya fi jan hankali kuma haka ake ganin lamarin zai kasance a fafatawar da za su yi ranar Asabar inda City za ta karbi bakuncin Liverpool.

Baya ga kasancewarsu kungiyoyin da ke kan gaba a Gasar Firimiya, maki daya da ke tsakaninsu a gasar ta Firimiya na daga cikin ababen da za su sa wasan da za a yi karfe daya da rabi na rana agogon Nijeriya ya ja hankalin jama’a.

Cikin ‘yan shekarun nan kungiyoyin biyu sun yi takarar lashe Gasar Firimiya sau uku yayin da suka buga wasan karshe na Gasar Zakarun Turai sau daya.

Kungiyoyin za su kece raini a Etihad inda kowannensu zai nemi darewa saman teburin Gasar firimiya.

Bugu da kari ana ganin karawar tasu za ta kasance karawar koca-kocai biyu da suka fi suna a Gasar Firimiya ne.

Yaya karawar za ta kasance?

Da yake bayani ga manema labarai ranar Juma’a, kocin City Pep Guardiola, ya ce yana son ganin yadda kulob dinsa zai fafata da kungiyar da ya kira “babban kulob.”

Sai an buga wasan kafin a san wa zai cigaba da kasancewa a saman teburin Gasar Firimiya tsakanin kungiyoyin biyu:Hoto/Getty Images

"Babban kulob, babbar kungiya. Ina maraba da wasan. Abin yabo ne a ce har yanzu Liverpool da Manchester suna nan," a cewarsa.

"Trent Alexander-Arnold zai iya buga wasan tsakiya a yanzu, amma dabarun daya suke. Sun kasance abokan hamayyarmu da suka fi girma.

Shi kuwa kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya shaida wa manema labarai cewa karawa da City daya ne daga cikin wasanni mafi wahala da za su buga.

"Ban sani ba game kasancewa abokan adawa. Amma a ganinmu na fagen wasa wannan daya daga cikin mawuyacin wasannin da mutum zai iya bugawa cikin shekaru, me yiwuwa tun lokacin da na zao nan,” in ji Klopp.

Ya ce tun da dai ‘yan wasan yanzu suke dawoywa daga hutun wasannin kasashe, sai an yi atisaye tukunna kafin ya san da wa da wa za su buga wasan.

TRT Afrika