Manchester United ta yi nasarar kai bantenta bayan da ta doke kulob din da ke tashen cin wasa a Gasar Firimiya, Aston Villa, da ci 3-2 a filin wasan Man U na Old Trafford, a jiya Talata.
Aston Villa ce ta fara zuwa kwallo a minti na 21 ta hannun dan Scotland, John McGinn kafin daga bisani dan wasan Villa dan asalin Belgium, Leander Dendoncker ya kara ta biyun bayan mintuna biyar.
An tafi hutun rabin lokaci Man United ba ta da ko kwallo daya. Amma bayan an dawo sai wasa ya sauya. Sai dai ƙwallon da dan asalin Agentina Alejandro Garnacho ya ciyo wa United a minti na 48 bai samu amincewar alkalin wasa ba.
Sai a minti na 59 Garnacho ya zura halastacciyar kwallo, bayan da Rashford ya ba shi fasin. Haka nan ya sake zura kwallo ta biyu a minti na 71 inda wasa ya koma kunnen doki biyu da biyu.
Man U ba ta fid da ran karasa cin yakin ba, inda a minti na 82, dan wasan gaba dan asalin Denmark, Rasmus Hojlund, wanda ya kwan biyu bai ci kwallo ba, ya samu nasarar zura kwallo ta uku, inda ya sa masoya United suka barke da kuwwa.
Haka dai wasa ya tashi man U na da galaba da ci 3 da 2, wanda ya sanya ta haye mataki na shida a teburin Firimiya bayan ta tattara maki 31 daga wasanni 19.
Wannan nasara za ta kara wa 'yan wasan United da manajansu Erik Ten Hag karfin gwiwa. Wasansu na gaba za su kara ne da Nottingham Forest, da ke kasan teburi. Sai kuma a 14 ga watan Janairu su kara da Tottenham da ke saman teburi.
Da ma dai ƙididdiga ta nuna cewa gabanin wasan Man U da Aston Villa, United ba ta taba rashin nasara a wasanni uku a jere ba, a duk wasanninta na gida, tun a watan Oktoba na shekarar 1962.