Kudus ya ce zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya burge 'yan kallo da magoya bayansa kungiyar./Hoto:Getty

Kungiyar kwallon kafa ta West Ham ta kammala sayen dan wasan tsakiyar Ajax Mohammed Kudus a kan kimanin $48m.

Kudus ya zura kwallo 19 sannan ya taimaka aka zura kwallo bakwai a dukkan gasar da ya buga wa Ajax a kakar wasan da ta gabata, ciki har da kwallayen da ya zura a ragar Liverpool da Napoli a Gasar Zakarun Turai.

"Tun ina karamin yaro nake fatan buga tamaula a dukkan gasa," a cewar Kudus, a yayin da West Ham ta tabbatar da isar sa Gasar Firimiya.

"Ina matukar jin dadin zuwa na nan. Amma ba iya nan zan tsaya ba, ina son samun ci-gaba. Na zaku na soma murza leda."

Kudus ya ce zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ya burge 'yan kallo da magoya bayan kungiyar.

Dan kasar ta Ghana ya soma murza leda ne a kungiyar kwallon kafar Nordsjaelland ta kasar Denmark a 2018, sannan ya tafi Ajax a 2020.

TRT Afrika