A daren jiya ne aka buga wani wasan hamayya tsakanin Liverpool da Everton, waɗanda suke yanki guda a Ingila, a wani wasa na Gasar Firimiya da ya yi zafin da har aka samu hatsaniya, kafin aka ƙare wasan da ci 2-2.
Wasan da shahararren alƙalin wasa ɗan Ingila, Michael Oliver ya jagoranta, ya gudana ne a gidan Everton a filin wasa na Goodison Park, tsakanin ƙungiyoyin da maki 30 ke tsakaninsu.
Liverpool ta je wasan tana mataki na ɗaya a saman teburin gasar, da maki 56, inda ta samu maki na 57. Ita kuwa Everton ta ƙare wasan tana mataki 15 da maki 27.
A minti na 11 Beto na Everton ya ciyo ƙwallon farko kafin Alexis Mac Allister ya rama wa Liverool a minti na 16.
Muhammed Salah ya bai wa Liverpool tazara da ƙwallo ta biyu a minti na 73.
Amma sai a minti na 8 bayan ƙarewar lokacin wasan, sai Everton ta farke ta hannun James Tarkowski aka tashi 2-2.
Hatsaniya ta ɓarke bayan nan har aka sallami 'yan wasan ƙungiyoyin biyu, Curtis Jones na Liverpool da Abdoulaye Doucoure na Everton.
Ƙorafin kyaftin ɗin Liverpool
Kyaftin ɗin Liverpool, Virgil van Dijk ya yi iƙirarin cewa alƙalin wasan, Michael Oliver ya gaza kula da wasan yadda ya dace inda har 'yan wasa suka yi ta hatsaniya bayan an tashi daga wasan.
Murnar farke ƙwallon da Everton suka yi ya janyo rigima tsakanin Abdoulaye Doucoure da masoya Liverpool.
Curtis Jones na Liverpool ya tunkari ɗan wasan inda 'yan wasa da magoya baya suka fara artabu kafin jami'an fili da 'yan sanda su shiga tsakani.
Alƙali wasa, Michael Oliver ya ba da jan kati ga Doucoure da Jones, sannan ya juya kan kocin Liverpool, Arne Slot da mataimakinsa Sipke Hulshoff saboda tunkarar alƙalin wasan.
Da yake magana da tashar TNT Sport, kyaftin ɗin Liverpool, Van Dijk ya ce, "Kowa ya ga yadda suka yi murnar cin ƙwallo, kuma damarsu ce".
Amma ya soki alƙalin wasan saboda gazawarsa wajen hana rigimar.
Ya ce, "Ina tunanin Doucoure ya so ya tunzura masoyanmu kuma Curtis bai ga dacewar hakan ba.... Ina ganin alƙalin bai iya shawo kan wasan ba."
Ƙauracewa taro
Kocin Liverpool ya soke halartar manema labarai na bayan wasa. Kocin da mataimakansa sun ƙi zuwa wajen taron.
Hakan ya faru ne saboda jan katin da aka ba su, wanda ya haramta musu gabatar da jawabi ga 'yan jaridun, inda aka bar kocin Everton David Moyes ya yi nasa jawabin.
Sakamakon jan katin da aka ba wa koci Slot da mataimakinsa Hulshoff, mai horar da 'yan wasan Liverpool Johnny Heitinga, wanda tsohon ɗan wasan Everton ne shi zai jagoranci Liverpool a wasansu na gaba da Wolves ranar Lahadi.