Haziƙin ɗan wasan Real Madrid ɗan asalin Brazil, Vinicius Jr ya ƙi amincewa da tayin da aka yi masa na jonewa da Cristiano Ronaldo a gasar Saudi Pro ta Saudiyya.
Rahotanni sun nuna cewa Vini na da burin lashe kyautar Ballon d'Or tare da Real Madrid, kuma hakan ne ya hana shi amsa gwaggwaɓan tayin da aka yi masa.
Tauraruwar Vincius tana haskawa a Madrid, inda yake kan gaba wajen tallafa wa kulob ɗin wajen lashe kofuna a gasannin La Liga da na Zakarun Turai.
A Real Madrid, Vini yana sanya riga mai lamba 7, wadda ita ce lambar gwarzon ɗan wasan duniya Cristiano Ronaldo, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau biyar.
Yayin da Ronaldo yake shekara ta biyu a Saudiyya, ƙungiyoyin ƙasar na ƙoƙarin kawo wani sabon haziƙin ɗan wasa, inda The Athletic ta ruwaito cewa wata tawagar Saudiyya ta tuntuɓi wakilan Vini game da yiwuwar ɗauko shi.
Da Vinicius ya zaɓi komawa Saudiyya, da zai zamo babban ɗan wasan da ta yo kamu a kakar bana. Saudiyyar dai na da burin haɓaka ƙwallon ƙafa gabanin shirye-shiryen maraba da Gasar Kofin Duniya ta 2034.
Shekarun Vinicius 24, kuma kwantiraginsa ba za ta ƙare a Real Madrid ba har sai shekarar 2027.