Yayin da Real Madrid ke shirin ɗauko babban ɗan wasan PSG Kylian Mbappe,ƙungiyar tana iya sakin Vinicius Junior ga manyan kulo-kulob da ke zawarcin sa.
Duba da yadda manyan ƙungiyoyin duniya ke neman Vinicius Jr. alamu sun nuna cewa Chelsea, Liverpool, da PSG sun shirya zuba maƙudan kuɗi don sayo shi.
A bazarar bana ne ake sa ran Vinicius zai sauya sheƙa kamar yadda jaridar El Debate ta ambato. Ƙungiyoyin suna kallon cewa tun da Mbappe za so Real Madrid, to dama ce gare su na dauko dan wasas.
Vinicius wanda ɗan asalin Brazil ne, kuma wanda ya samu damar yin zarra a kakar bana, inda ya buga wasanni da yawa kuma ya zama abin dogaro wajen koci Ancelotti, da alama ba zai juri yin takara da Mbappe wajen samun gurbin wasa ba.
Mbappe da Vinicius duka matasa ne masu jini a jika, don haka PSG ta Faransa da kuma Liverpool da Chelsea a Ingila suna shirin tayin kudin da ake ce ya kai EUro miliyan €200 million (wato dala miliyan $217m).