Kroos ya cika shekaru goma yana buga wa Real Madris wasa. / Photo: AA

Gwarzon ɗan wasan tsakiya na Real Madrid, Toni Kroos ya sanar da cewa zai bar ƙungiyar kuma ya yi ritaya daga buga ƙwallon ƙafa kacokan, da zarar an kammala gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024.

Kroos ya sanar da wannan ne a matsayin wani hukunci da ya yanke bisa raɗin-kansa, inda ya ce gasar ta Euro 2024 ita ce za ta zamo wasansa na ƙarshe a matsayin ƙwararren ɗan ƙwallo.

Sai dai kafin nan, Kroos zai cigaba da wasa tare da Real Madrid, inda za su buga wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai, ranar 1 ga watan Yuni, inda za su kara da Borussia Dortmund a birnin Landan.

Toni Kroos ya faɗa cewa, “Ranar 17 ga watan Yuli na 2014, ranar da aka gabatar da ni a Real Madrid, rana ce da ta sauya min rayuwa. Rayuwata a matsayin ɗan ƙwallon ƙafa, har da ma rayuwata a matsayina na ɗan-adam”.

Bayan cika shekaru 10 a Madrid, Kroos ya gode wa masoya kulob ɗin, daga nan sai ya ce, "Wannan na nufin aikina na ɗan ƙwallon ƙafa zai zo ƙarshe a bazarar nan bayan gasar Euro”.

Kroos ɗan asalin Jamus ne mai shekaru 34. Yana cikin tawagar Jamus da ta lashe kofin duniya na FIFA a 2014, kuma sau 106 yana buga wa tawagar Jamus wasa.

A watan Yuli 2021 ya sanar da ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa, amma a watan Fabrairun 2024 ya sanar da cewa zai dawo ya buga wa Jamus wasa a gasar Euro 2024, bayan da kocin Jamus Julian Nagelsmann, ya neme shi.

Za a buga gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024 daga 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yuli a Jamus.

TRT Afrika