Shekarun Ruud van Nistelrooy 48n a duniya. / Hoto: Reuters 

Ruud van Nistelrooy, tsohon ɗan wasan Manchester United ya karɓi aikin horar da 'yan wasan tsohuwar ƙungiyar tasa, inda zai yi aiki da manajan ƙungiyar, Erik ten Hag a kakar da za a fara a wannan watan.

Lokacin da yana buga wa United, ya ci ƙwallaye 150 cikin kakar wasanni biyar. Sannan ya zamo kocin PSV a gasar Eredivisie ta Holland, a shekarar 2022 zuwa 2023.

Van Nistelrooy ƙasarsu ɗaya da Ten Hag, kuma za su yi aiki tare, inda wasu masana ƙwallo kamar wani tsohon ɗan wasan United, Dwight Yorke ke ganin Nistelrooy ya kama hanyar karɓe kujerar Ten Hag.

Dwight Yorke ya faɗa cewa, "A fili yake ga kowa a Manchester United cewa idan aka sallami Erik ten Hag, to za a naɗa Ruud van Nistelrooy.”

Sai dai Yorke ya yi sharhi kan matakin United na kawo mutumin da zai iya barazana ga aikin Ten Hag, duk da cewa sun tsawaita masa kwantiragi.

Ya kuma ƙara da cewa "A ƙashin gaskiya, ya fi kyau a ce mutum ya tsaya a gefe idan yana da burin zama cikakken manajan ƙungiya."

Erik ten Hag ya jagoranci United wajen lashe Kofin FA a kakar bara, baya ga cewa ya ciyo wa United Kofin Carabao a shekarar da ya zo kulob ɗin.

Sai dai ana yawan yin tababa kan zamansa, duk da a yanzu kwantiraginsa ba zaI ƙare ba sai a bazarar 2026.

TRT Afrika