Ruben Amorim

Hukumomin Manchester United sun tabbatar da tafiyar Ruud van Nistelrooy kocin da ya yi wa ƙungiyar riƙon ƙwarya na 'yan makonni, tare da mataimakansa guda uku, yayin da sabon koci Ruben Amorim ya iso yau Litinin.

Sanarwar da United ta wallafa a shafinta ta ce Nistelrooy zai cigaba da zama gwarzon ƙungiyar, kuma "Muna godiya da taimakonsa da kuma yadda ya yi aikinsa iya zamansa a kulob ɗin".

Sauran jami'an horar da 'yan wasa da suka bar United sun haɗa da Rene Hake, Jelle ten Rouwelaar da Pieter Morel. A yanzu United ta ce za ta sanar da jerin sabbin jami'an horar da ƙungiyar a nan gaba.

Yayin da sabon kocin Manchester United, Ruben Amorim yake isowa Old Trafford Litinin 11 ga Nuwamba, don fara aiki, masoya United za su kewar van Nistelrooy, wanda ya rike ƙungiyar tsawon wasanni huɗu bayan an sallami Erik ten Hag.

Tuni wasu masoya United da masu sharhi kan ƙwallo ke cewa ko ba komai Nistelrooy ya cancani zama a muƙami na biyu a ƙungiyar, ganin yadda ya jagoranci United wajen lashe wasanni uku da yin canjaras sau ɗaya.

Tawagar Amorim

A baya Nistelrooy mai shekaru 38, ya taɓa cewa zai zauna a United tare da sabon koci. Kuma nasarar da ya samu a ɗan lokacin da ya yi ruƙo ta saka fatan cewa yana hazaƙa da fahimtar ƙungiyar da ya taɓa bugawa wasa a baya.

Van Nistelrooy ɗan Netherland ne kuma gwarzo a tarihin tsaffin 'yan wasan Man United. Shekaru kusan 20 bayan barinsa a matsayin ɗan wasa, ya dawo ƙungiyar da bazarar bana, a matsayin mai taimaka wa Ten Hag horar da 'yan wasa.

Sai dai tuni sabon koci Amorim mai shekara 39 ya bayyana wa mahukuntan United cewa yana son mataimakansa a tsohon kulob ɗinsa na Sporting CP, Emanuel Ferro, Adelio Candido, da sauran jami'an horo su biyo shi zuwa United.

Sai ranar 24 ga Nuwamba ne sabon kocin zai jagoranci Manchester United a karon farko a wasansu da da Ipswich Town, wanda zai zo bayan hutun wasannin ƙasashen.

TRT Afrika