Wannan ne karo na shida da Real Madrid ta ɗaga kofin Champions League a jere a wasannin ƙarshe 11 da suka gwabza./Hoto: Real Madrid C.F.

Real Madrid ta lashe gasar Zakarun Turai ta Champions League karo na 15 bayan ta doke Borussia Dortmund da ci 2-0 a fafatawar da suka yi a Wembley ranar Asabar.

Babu ƙungiyar da ta zura wa abokiyar hamayyarta ƙwallo har aka tafi hutun rabin lokaci, sai dai bayan an dawo ne ɗan wasan Madrid Daniel Carvajal ya ci ƙwallo a minti na 74 yayin da Vinicius Junior ya ci tasa ƙwallon a minti na 83.

Hakan na nufin Vinicius Junior ya ci ƙwallaye 11 sannan ya taimaka aka zura ƙwallo 11 a tarihinsa na gasar Champions League.

Dortmund ta samu damarmaki da yawa na cin ƙwallo amma hakan ya gagara.

Wannan ne karo na 15 da suka yi gumurzu a Champions League, inda Real Madrid ta yi nasara sau bakwai, yayin da Dortmund ta yi galaba sau uku.

Kazalika shi ne karo na biyu da Dortmund ta sha kashi a Wembley a wasan ƙarshe na Champions League, bayan da Bayern Munich ta doke ta 2-1 a shekarar 2013.

TRT Afrika da abokan hulda