Real Madrid na murnar lashe Kofin Copa del Rey karo na ashirin. Hoto/Getty

Vinicius Junior da Rodrygo sun taka muhimmiyar rawa a wasan da Real Madrid ta Copa del Rey karon farko tun 2014.

Madrid ta lashe Kofin ne bayan ta doke Osasuna da ci 2-1 a fafatawar da suka yi a filin wasa na La Cartuja ranar Asabar da daddare.

Rodrygo ne ya zura dukkan kwallayen a minti na biyu da minti na 70, yayin da Vinicius Junior ya taimaka masa suka kai ga nasarar lashe Kofin wanda shi ne karo na ashirin a tarihin kungiyar.

Dan wasan Osasuna Lucas Torró ne ya taimaka wa kungiyarsa ta ci kwallo daya a minti na 58.

Sai dai duk da goyon bayan da suka rika samu daga magoya bayansu 25,000 don ganin sun dauki wani babban Kofi a karon farko a tarihinsu na shekara 103, ba su yi nasara ba.

TRT World