Daga Charles Mgbolu
'Yan wasan kwallon kwando zarata ne, dogaye, masu karfin jiki, kuma sun gwanance wajen tsalle da direwa, da wulli, da yanka da bal cikin da'irar wasa.
Ranar Disamba 21, al'ummar duniya ke bikin Ranar Kwallon Kwando ta Duniya, don nuna fitaccen matsayin da wasan da 'yan wasan suke da shi.
A wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniya da ke murnanr ranar ta kwallon kwando a wannan shekaru, MDD ta bayyana muhimmancin wasan wajen sauya ‘tunani da janyo fahimtar juna tsakanin mabanbantan al'ummomi da siyasa.
Bisa la'akari da kiyasin Kungiyar Kwallon Kwando ta Duniya, a yau akwai akalla ;yan wasan kwallon kwando miliyan 450 a fadin duniya.
Duk da cewa wasan kwallon kwando bai kai farin jinin kwallon kafa ba a nahiyar Afirka, a zahiri yana da masoya da suka kai dubban daruruwa.
A wannan jerin, mun kawo bayanan 'yan Afirka shida daga kasashen Afirka shida, wadanda suka shahara a gasar kwallon kwando mafi girma a duniya, wato gasar NBA ta Amurka.
Giannis Antetokounmpo, Nijeriya
Giannis Sina Ugo Antetokounmpo (Adetokumbo), yana da shekara 29 a duniya, dan Nijeriya ne, kuma kwararren dan wasan kwallon kwando da ke bugawa kulob din Milwaukee Bucks a gasar Kwallon Kafa ta Amurka, NBA.
Antetokounmpo, wanda ke da fasfo din kasar Nijeriya da Girka, yana buga wa kulob din kasa na Girka, kuma ana masa lakabi da "Greek Freak" saboda hanzarinsa, da karfi, da iya juya kwallo.
Sai dai ya fada a tattaunawar da aka yi da shi cewa kasancewarsa tsatson dan Nijeriya da al'adun kasar yana matukar tasiri kansa.
Ana kallonsa a matsayin gwarzon dan wasan gaba kuma babban gwarzo daga nahiyar Turai da aka taba samu a tarihi.
An haife shi kuma ya girma a babban birnin Girka, Athens. Iyayensa 'yan Nijeriya ne kuma ya fara buga wasan kwallon kafa a kungiyar Filathlitikos ta Athens.
A shekarun 2016–17,ya zama dan wasa na farko da ya shiga jerin masu maki da yawa a jadawali 20 na rukunin maki, da tallafawa, da kwatowa, da tarewa.
A 2017, ya ci kyautar Dan Wasan da ya fi samun cigaba, sannan ya samu shiga jeri bakwai na Gwaraza, wanda ya hada da zama kyaftin din Gwaraza na shekarun 2019, 2020, da 2023.
Joel Embiid, Kamaru
An haifi Embiid a ranar 16 ga watan Maris na 1994. Kwararren dan wasa ne dan kasar Kamaru kuma yana buga wa kungiyar Philadelphia 76ers a gasar NBA.
Kamar Antetokounmpo, shi ma Embiid yana da shedar zama dan kasa guda biyu (Faransa da Amurka).
Embiid yana da tsawon kafa-7 (mita 2.1), kuma sau shida yana cin kyautar Gwarzon NBA, kuma sau biyar ana saka shi jerin mambobin hadaka na gwarzayen NBA, sannan sau uku yana shiga jerin gwarazan masu tsaron gida. An ayyana Joel Embiid a matsayin dan wasan NBA Mafi Daraja na shekarar 2023.
Yana wa kansa lakabi da "the process", kuma yana cikin masu cin kwallo na gaba-gaba a gasar NBA a kakar 2021–22 da 2022–23.
Clint Capela, Angola, Jumhuriyar Dimukradiyyar Congo
An haifi Capela a birnin Geneva, na Switzerland, kuma mahaifinsa dan Angola ne sannan mahaifiyarsa 'yar Congo ce.
A shafin bayanansa, ya ce ya fara sha'awar kwallon kwando bayan haduwa da shahararren dan kwallon kwando na kasar Swisszerland, Thabo Sefolosha.
Yana dan shekara 15, aka gano shi yayin wasan Karamin Matakin na Turai lokacin da yake bugawa kungiyar kasar Swisszerland. Daga nan ya shiga cibiyar horo ta Chalon-sur-Saône, a INSEP, da ke Faransa.
Ranar 19 ga Nuwamban 2016, Capela ya ci maki 20 a wasan da suka yi nasara da 111-102 kan kungiyar Utah Jazz.
A 27 ga Nuwamban 2016, ya kafa tarihin maki 21 a wasan da suka kara da Portland Trail Blazers.
A yanzu Capela yana buga wa kungiyar kasa ta Swisszerland.
Dennis Schröeder, Gambia
Dennis Mike Schröder (wanda aka haifa 15 ga Satumban 1993) mahaifinsa dan Jamus ne, amma mahaifiyarsa 'yar Gambia.
A baya ya buga wa kungiyar SG Braunschweig da Phantoms Braunschweig a Jamus, kafin ya kwashe kaka biyar a gasar NBA yana buga wa kungiyar Atlanta Hawks, sannan ya yi shekara biyu da kungiyar Oklahoma City Thunder.
Shi ne ya mallaki kungiyar Basketball Loewen Braunschweig ta Jamu da ke buga gasar Basketball Bundesliga, kuma ya shi ne babban mai hannun jari a kungiyar tun shekarar 2018.
A 2023, ya taimaka wa kungiyar kasa ta Jamus suka ci Kofin Duniya a karon farko, a gasar Kofin Duniya ta Kwallon Kwando ta FIBA. Sannan a ayyana shi a matsayin Dan Kwallo Mafi Daraja a gasar.
Bol Bol, Sudan ta Kudu
Bol Manute Bol dan shekara 24, kuma yana da asali a Sudan ta Kudu da Amurka. Kwararren dan wasan kwallon kwando da aka haifa a Khartoum, na Sudan, kuma ya fara rayuwa a birnin Kansas City, na Amurka tun yana karami.
Yana buga wa kungiyar Phoenix Suns ta gasara NBA kuma da ne ga tsohon dan wasan kwallon kwando marigayi Manute Bol (wanda ya yi suna a matsayin mafi tsayi a gasar NBA a tarihi).
Tsayinsa ya kai kafa-7 da inci 3 (mita 2.21), Bol a yanzu yana daya daga cikin mafi tsayi a gasar NBA.
An saka Bol a matsayin na 44 cikin 'yan wasan Miami Heat a gasar NBA ta kakar 2019.
Ranar 1 ga Janairun 2022, Bol ya ci maki 11 tare da kwatowa uku, a wasan da suka buga da Houston Rockets inda aka tashi 124-111.
Georges Niang, Senegal
Niang da ne ga Sidy da Alison Niang. An haifi babansa a Senegal.
An ayyana shi a matsayin dan wasa mafi fice a gasar, bayan ya ci maki 23 a 11-na-11 bugu daga fili a gasar NEPSAC Class AA na 2011.
An dauki Niang a matsayin daya daga fitattun 'yan wasa a gabar Gabashin Amurka, kuma ya shiga jerin mutum 100 na kasa.
Ana wa Niang lakabi da ''The Minivan'' kuma ya zarta maki 2,000-point a babbanm sakandare, inda ya ci matsakaicin maki 20.2 a 6.2 kwatowa a duk wasa.
Kuma shi ne dan wasa na farko da ya cimma gasa huda a jere a NCAA.
A 23 na Yunin 2016, an zabi Niang a kungiyar Indiana Pacers a shekarar 2016 na gasar NBA, kuma ranar 6 ga watan Yuli na 2023, Niang ya shiga kwantiragi da Cleveland Cavaliers inda ya ci gaba da wasa.