Yayin da ake raɗe-raɗin cewa Manchester United na neman yadda za ta ɗauko tauraron ɗan wasa ɗan asalin Nijeriya, Victor Osimhen, a yanzu zancen ya kusa tabbata saboda wani raɗe-raɗin na tafiyar ɗan wasansu Marcus Rashford.
Rashford, wanda ɗan wasan gaba ne a Man U, ya samu saɓani da sabon kocin ƙungiyar Ruben Amorim, inda kocin ya daina saka shi a wasa a karo uku a jere cikin sati guda.
Shi kansa ɗan wasan ya bayyana aniyarsa ta barin ƙungiyar don neman wata, abin da ya ƙara girman raɗe-raɗin tafiyar tasa.
A kwanakin nan ne shafin Sky News ya rawaito cewa ƙungiyar ta nuna sha'awar ɗauko ɗan wasan da yake ƙungiyar Napoli ta Italiya, wanda a halin yanzu yake aro a Galatasaray ta Turkiyya.
Yayin da ake sa ran tafiyar Rashford a Janairu mai kamawa lokacin da za a buɗe kasuwa cinikin 'yan wasa, ana kallon hakan a matsayin babbar damar zuwan Victor Osimhen.
An tuntuɓi Osimhen
Osimhen dai zaƙaƙurin ɗan wasan gaba ne, maci ƙwallo, inda yake wuta a halin yanzu bayan zuwansa babbar ƙungiyar ta Istanbul. Ya ci ƙwallaye 12 a wasanni 15 da ya buga a kakar bana.
Rahotannin na cewa tuni jami'an United ne suka fara tuntuɓar wakilan Osimhen kuma matakin da suke kai shi ne na samun matsaya tare da ɗan wasan.
Sai dai akwai babban ƙalubale na yadda za ta kaya da uwar ƙungiyarsa Napoli, waɗanda za su nemi farashin da ya kai euro miliyan €75 (dala miliyan $77).
Zuwan Osimhen Man United zai iya biyan buƙatar sabon koci Amorim, wanda ke fafutukar sake fasalin ƙungiyar, wadda ta yi rashin nasara a wasanni uku cikin huɗu da suka buga a gasar Firimiya.