Magoya baya da jami'an kungiyar galatasaray ne suka tarbi Osimhen a filin jiragen sama. Photo: AA

Ɗan wasan gaba na Nijeriya Victor Osimhen ya isa Istanbul, Turkiyya, don kammala tattaunawar dawowarsa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray SK daga Napoli.

Galatasaray ta ƙudiri niyyar ƙara Osimhen a tawagar 'yan wasanta bayan kammala Gasar Premier ta Ingila da Rufe Sayen 'Yan wasa a Saudiyya inda aka gaza sayen ɗan wasan gaban mai shekara 25.

Bidiyon da aka fitar a shafukan sada zumunta ya nuna Osimhen na daga hannaye ga magoya baya da ke kaɗa tutar Galatasaray a yayin tarbarsa a filin jiragen sama ranar Litinin da daddare.

"Victor Osimhen ya iso Istanbul," in ji wani saƙo da Galatasaray ta fitar ta shafin X.

"Yanayin na da matuƙar kyau. Magoya baya mafi nagarta a duniya na nan wajen. Na ji daɗin kasancewa ta a nan. Ina farin ciki sosai. Na zaƙu na ga magoya baya a filin wasa. Zan yi musu iya ƙoƙarina," in ji Osimhen a gajeren bayanin da ya yi a filin jirgin saman.

Ɗan wasan gaban ya bar filin jirgin a wata mota ta musamman tare da Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Galatasaray Ibrahim Hatipoglu da Daraktan Ƙwallon Ƙafa Cenk Ergun.

TRT Afrika