Chelsea da Napoli sun kasa cim ma matsaya kan ɗan wasan na Nijeriya. / Hoto: Reuters

Ɗan wasan gaban Nijeriya Victor Osimhen zai ci gaba da zama a Napoli bayan kasa cim ma matsaya tsakanin ƙungiyar da Chelsea.

Yunƙurin komawar ɗan wasan zuwa Stamford Bridge domin ci gaba da taka leda ya bi ruwa sakamakon an rufe kasuwar cinikayyar ‘yan wasa a Ingila ba tare da ɓangarorin sun ƙulla wata yarjejeniya ba.

Rahotanni sun ce tattaunawar ta wargaje ne sakamakon kuɗin da Chelsea ta yanka za ta rinƙa bai wa Osimhen ba su kai kuɗin da yake samu a halin yanzu a Napoli ba.

Sai dai ana ganin makomar ta Osimhen a halin yanzu ba ta da tabbaci domin komai zai iya faruwa ganin cewa kulob ɗin Al-Ahli na Saudiyya na zawarcin ɗan wasan Nijeriyar mai shekara 25.

Ta wani ɓangaren za a iya cewa ɗan wasan na Nijeriya na da damar zuwa Al-Ahli sakamakon har zuwa ranar Litinin kasuwar cinikayyar ‘yan wasa ta Saudiyya na nan a buɗe.

Sai dai kuma a wani ɓangaren kuma Osimhen ɗin zai kasance a tsaka mai wuya bayan kulob ɗin na Saudiyya ya sayi ɗan wasan gaban Ingila Ivan Toney.

Rahotanni sun ce tuni ƙungiyar Brentford ta karɓi kuɗin cinikin na Toney wanda aka yi kan fam miliyan 40.

Idan ta tabbata kulob ɗin na Saudiyya bai sayi Osimhen ba, ana fargbar zai iya ɗumama benci a Napoli har zuwa watan Janairu lokacin da za a sake buɗe kasuwar cinikayyar 'yan wasan.

TRT Afrika da abokan hulda