Alvaro Morata  ya ci kwallayen ne a minti na hudu da kuma minti na 46./Hoto: Reuters

Alvaro Morata ya zura kwallo biyu a wasan hamayya da Atletico Madrid ta casa Real Madrid da ci 3-1 a gasar LaLiga ranar Lahadi.

Morata ya ci kwallayen ne a minti na hudu da kuma minti na 46 yayin da Antoine Griezmann ya zura kwallo a minti na 18 a fafatawar da suka yi a Wanda Metropolitano.

Sai dai Toni Kroos ya taimaka wa Real Madrid inda ya ci mata kwallo daya.

Wannan nasara ta sa Atletico ta zama ta biyar a teburin La Liga, yayin da Real take mataki na uku - a bayan Barcelona da Girona - bayan ta yi asarar maki a karon farko a wannan kakar wasan.

Ga sauran sakamakon wasan La Liga na ranar Lahadi:

Real Sociedad - Getafe: 4-3

Rayo Vallecano - Villarreal: 1-1

Las Palmas - Granada: 1-0

Real Betis - Cadiz: 1-1

TRT Afrika da abokan hulda