Ethan Nwaneri haifaffen Ingila ne, amma mahaifansa 'yan Nijeriya ne. / Hoto: Reuters

Matashin ɗan wasan Arsenal, Ethan Nwaneri ya samu shiga babbar tawagar ƙungiyar, inda har ya buga manyan wasanni a Gasar Firimiya, da Zakarun Turai, da Carabao, kuma ya ci ƙwallaye.

Sai dai duk da ƙokarin da yake nunawa, har yanzu ba a sahale masa ya shiga ɗakin da sauran tawagar Arsenal ke sauya tufafi kafin fara wasa ba, da kuma lokacin hutun rabin lokaci.

Hakan na faruwa saboda tanadin dokar da ya haramta wa 'yan wasa da ke da shekaru ƙasa da 18 shiga inda 'yan wasan babbar tawagar ke shirya wa wasa.

Shi kansa kocin Arsenal, Mikel Arteta ya bayyana cewa abin yana ɗaure masa kai, duba da yadda haziƙin ɗan wasan ke taimaka wa tawagar matuƙa.

Arteta ya faɗa wa manema labarai cewa, "Har yanzu Ethan ba zai iya shiga ɗakin sauya kaya na 'yan ƙungiyarmu ba, kuma hakan yana ban mamaki. Dole sai dai ya je wani wajen ya sauya kaya".

Tsatson Nijeriya

Mai shekaru 17, Nwaneri haifaffen Ingila ne, amma mahaifansa 'yan Nijeriya ne. Kuma ya samu horo a makarantar koyar da ƙwallo ta Arsenal tun yana ƙarami.

Tun bayan samun shiga babbar tawagar Arsenal, Nwaneri ya ba da gudunmawa sosai a tawagar, inda yake buga wasa a gaba ɓangaren dama.

Ranar Lahadin da ta gabata a wasan Arsenal da Manchester City na Gasar Firimiya, Nwaneri ya ci ƙwallo ta biyar da suka ci, a wasan da aka tashi 5-1.

Haka ma a wasansu na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai da suka buga da Girona, Nwaneri ya ci ƙwallo ta biyu a minti na 42, wanda ta ba su nasara a wasan da ci 2-1.

TRT Afrika