Manajan kungiyar Manchester United Erik Ten Hag ya tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo ya ki zuwa a matsayin wanda za a ajje a benchi a lokacin da suka buga wasa da yin nasara kan Tottenham, kuma z a aga abun da zai biyo baya.
Tattaunawar bayan wasan da aka samu nasara da ci 2 da 0 kan Tottenham a Old Trafford a ranar Laraba ya zama batun saurin fitar da dan wasan na Portugal mai shekaru 37 ya yi.
Ronaldo ya fita daga wasan kafin a busa kusur din tashi, kuma ya bar filin Old Trafford da wuri.
A ranar Alhamis United ta sanar da saboda abun da dan wasan ya yi, an cire sunansa daga ‘yan wasan da za su taka leda a waan da za a yi da Chelsea.
Da aka tamye shi yayin tattaunawa da ‘yan jarida kan ko Ronaldo ya ki zuwa wasan ne da Tottenham saboda an ajje shi a benchi, sai ya ce “Eh”.
Ten Hag ya ce “Abun da ya faru a maganganun tsakani na da Ronaldo ne. Sanarwar ai a bayyane take ina tunanin hakan.”
Amma manajan na Holan, a zagayen farko na zaman sa a Old Trafford, Ronaldo ya zama mai matukar mhimmanci a kungiyar.
Dan wasan na gaba na daga cikin ‘yan wasan da suka bar Old Trafford da wuri watan Yuli a lokacin wasan share fage tsakaninsu da Rayo Vallecno, wanda ya sanya Ten Hag ya zayyana muhimmancin ‘yan wasa su zauna su goyi bayan abokansu.
Da aka tambaye shi kan yadda ya yi da yanayin, sai dan kasar Holan a ranar Juma’a ya bayyana cewa “Ya muka yi, ni ne Manaja. Ni ne ke da alhakin aiyukan wasanni a nan, dole ne na saka ka’idoji da dokoki, kuma dole ne na kula da an yi aiki da su.”
Ya ce “Muna cikin kungiya ne. Saboda haka muna da dokoki, muna da ka’idoji kuma dole ne na kula da an yi aiki da su. Bayan Rayo Vallecano, na fada maka ba abun da za a mince da shi ba ne, amma ba shi kadan ba ne. Abu ne da ya shafi kowa.”
Idan ya sake yin hakan a karo na biyu, zai karbi sakamakonsa. Hakan ne abun da muka yi. Gobe za mu yi kewar sa. Wannan kewa ce tamu. Rashi ne a wajen tawagar.
Manajan ya ci gaba da cew “Amma Ina tunanin hakan na da muhimmanci ga halayyar tawagar. Yanzu mun mayar da hankali kan Chelsea, hakan na da muhimmanci.”
Zafafar lamarin
Ronaldo ya mayar da mrtni kan cire shi daga ‘Yan wasan da za su buga wasa a farkon wasa iinda ya ce, ya yi hakan ne saboda zafafar zuciyarsa.
A sakon da ya fitar ta shafinsa na Instagram, ya ce “A koyaushe ina kokarin bayar da misali ga matasa masu tasowa da nake wakilta. Abun takaici abu ne da ba zai yiwu a koyaushe ba, a wani lokacin zafin na haifar da abu mafi kyau gare mu.”
Ya kara da cewa “A yanzu haka ina jin ya kamata na ci gaba da aiki a Carrington, goya baya ga ‘yan tawagata na kuma shirya tunkarar komai a kowanne wasa.”
“Matsin lamba ba zai taba zama maslaha ba. Bai taba zama ba kuma. Wannan Manchester United ce, idan muka hade ne za mu yi nasara. Da sannu za mu sake tafiya tare.”
Tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus ya jefa kwallaye 24 a wasannin da ya bga a 2021/2022 inda a nan ma ya kafa tarihi a matsayin zakaran duniya
Amma bai j dadin yadda Manchester United ba ta samu damar halartar Gasar Zakarun Turai ba, ya yi kokarin barin Old Trafford amma hakan ba ta yiwu ba.
Ronaldo da ya lashe Gasar Zakarun Turai sau biyar tare da Real da United, ya fara buga wasanni biyu na gasar Premier ta Ingilaa wannan kakarwasannin kuam ya jefa kwallo daya kawai a gwagwarmayar ta Ingila.
Dan wasan dan gaba da bai samu damar halartar ziyarar Australia da Taylan da kungiyar United ta yi ba, a lokacin da Ten Hag ya maye sunansa a wasan makon karshe da za su yi da Newcastle.