Yanzu Galatasaray tana da maki daya a gaban Manchester United. / Hoto: Reuters

Makomar Manchester United a Gasar cin Kofin Zakarun Turai tana tangal-tangal bayan sun yi canjaras da ci 3-3 a fafatawar da ta yi da Galatasaray a ranar Laraba.

United tana da ci 2-0 a cikin minti na 18 da soma wasa inda Alejandro Garnacho da Bruno Fernandes suka zura kwallaye,

Daga bisani Galatasaray ta farke daya ta hannun Hakim Ziyech inda aka tafi hutun rabin lokaci, United na cin 2-1.

Bayan da suka dawo daga hutun rabin lokaci ne Scott McTominay ya ci wa United kwallo na uku.

Galatasaray ta ci karin kwallo biyu ne ta hannun Muhammed Kerem Akturkoglu da Hakim Ziyech abin da ya bai wa kungiyar ta kasar Turkiyya maki daya a gaban United, wacce take a karshe a rukunin nasu.

Dole ne Manchester United ta doke Bayern Munich a wasan karshe na Rukunin A idan ba haka ba ta yi bankwana da gasar Zakarun Turai.

An sanya wata katuwar tuta da aka rubuta “Sannu da Zuwa Cikin Bala'i” a wani gefe na filin wasan Ali Sami Yen gabanin soma wasan, don tuna wa 'yan wasan United irin abin da magoya bayan Galatasaray suka yi musu a filin jirgin Istanbul shekru 30 da suka wuce kafin su soma wasan gasar Zakarun Turai.

TRT Afrika