Manchester City ta fitar da rahoton kudin shigar da ta samu a shekarar 2022/2023 wanda ya kai fam miliyan 712.8.
Hakan ya nuna cewa kungiyar ta samu karin fam miliyan 99.8 a kan kudin shigar da ta samu a bara sannan ya zarta £648.4m da kishiyarta Manchester United ta samu a shekarar kudi ta 2022/2023 .
Kazalika City ta samu ribar £80.4m, wato kari kan £41.7m da ta samu a bara.
Kungiyar ta fitar da wannan sanarwa ce a shekarar da ta lashe kofuna uku, wato Kofun Gasar Firimiya da na FA da kuma na Zakarun Turai, inda ta kasance ta biyu da ta dauki kofuna uku a kakar wasa daya bayan Manchester United wadda ta yi irin wannan bajinta a 1999.
Rahoton kungiyar ya nuna muhimman hanyoyin uku da ke samar mata kudaden shiga da suka hada da kasuwancinta da watsa shirye-shirye da kuma tsare-tsarenta na gudanarwa.
A bara, an bai wa kungiyar lambar yabo ta kungiyar kwallon kafa mafi daraja a duniya a karon farko kamar yadda rahoton 2023 Brand Finance Football 50 ya bayyana, inda darajarta ta kai €1.51 b.
"A takaice dai, Manchester City ta samu gagarumar nasara a wasan kwallon kafa da kuma shekarar kasuwanci a tarihinta a kakar wasan bara," a cewar shugaban kungiyar Khaldoon al-Mubarak.