Marcus Rashford yana karɓar fam miliyan £365,000 duk sati, yayin da Harry Maguire ke karɓar fam miliyan £190,000 duk sati. / Hoto: Reuters 

Rahotanni daga Old Trafford, hedikwatar Manchester United a Ingila suna cewa mahukuntar ƙungiyar sun shirya tilasta wa ɗan wasan gaba Marcus Rashford barin kulob ɗin a Janairu mai zuwa.

Hakan zai faru ne sakamakon neman ‘sauya al'adar’ tawagar ƙarƙashin sabon koci Ruben Amorim, da kuma mamallakin ƙungiyar Sir Jim Ratcliffe. Da ma tuni aka sallami daraktan wasanni na ƙungiyar Dan Ashworth.

Rashford mai shekaru 27 yana fama da rashin tabbas a tagomashinsa yayin wasa, kuma a halin yanzu yana nuna gazawa a aikinsa, duk da a kakar bana ya ci ƙwallaye bakwai zuwa yanzu.

Jaridar The Guardian ta yi iƙirarin cewa za a saka Rashford a kasuwa, saboda mamallaka ƙungiyar, Sir Jim Ratcliffe da kamfanin INEOS sun yanke cewa ba za su “ɗauki tsohon kaya” ba a tafiyar sake gina Man United.

Ko a wasan Man U na ƙarshen makon jiya, Koci Amorim ya ajiye Marcus Rashford da abokin wasansa Alejandro Garnacho, saboda rashin nuna ƙoƙarinsu.

An ambato kocin yana kare matakin da ya ɗauka yana mai cewa, “Yana da muhimmanci ana duba ƙwazo a wajen atisaye, da ƙoƙari a wasa, da tufafin da kake sawa, yadda kake cin abinci, da yadda kake mu'amalantar abokan wasa, da yadda kake iza 'yan tawaga.”

Harry Maguire zama daram

Bayan da ɗan wasan baya na Man United, Harry Maguire ya taka rawar gani a wasan da United ta doke maƙwabciyarta Man City a ƙarshen mako, ɗan wasan ya samu yabo daga koci Ruben Amorim.

Maguire ya hana zaƙaƙurin ɗan wasan gaba na Man City Erling Haaland yin sakat a wasan nasu, wanda ya taimaka United ta yi nasara kan City da ci 2-1.

A yanzu dai rahotanni na cewa wakilan Maguire sun fara kykkyawar tattaunawa da mahukuntan ƙungiyar domin tsawaita kwantiraginsa.

Wannan ya sa ana kallon cewa Maguire mai shekaru 31 a duniya, ya shawo kan rashin ƙoƙarin da ya yi ƙaurin suna da shi a baya.

Tun a bazarar da ta gabata ne aka yi tunanin za a sallami Maguire daga United, saboda tarin lokutan da ya nuna rashin iya aiki a bana, musamman a ƙarƙashin tsohon Koci Erik ten Hag.

An taɓa raɗe-raɗin cewa Maguire zai koma West Ham, amma sai ya ci gaba da zama a ƙungiyar har ya ringa riƙe muƙamin kyaftin.

TRT Afrika