An yi rangwamen fam miliyan £20 a farashin Harry Maguire. / Hoto: AP

Shahararren mai tsaron gida a ƙungiyar Manchester United ta Ingila, wato Harry Maguire, ya fara shirin tattara komatsansa ya bar ƙungiyar.

A kakar cinikin 'yan wasa da za a buɗe a watan Janairun baɗi ne ake sa ran Man U za ta rabu da ɗan wasan nata ɗan asalin Ingila, wanda a yanzu rahotanni ke cewa an rage farashin da ake neman sayar da shi.

Tuntuni da ma Maguire ya rasa matsayi a tawagar da ke ƙarƙashin koci Erik Ten Hag, bayan da aka cire shi daga muƙamin kyaftin ɗin ƙungiyar a bara, inda Bruno Fernandes ɗan asalin Portugal ya maye gurbinsa.

An yi hasashen cewa Maguire zai koma taka leda a ƙungiyar West Ham tun a bara, amma sai hakan bai faru ba.

A yanzu dai an ruwaito mujallar Daily Star na cewa United za ta yi ƙoƙarin sayar da ɗan wasan mai shekaru 31 a Janairun baɗi, kuma ta zaftare farashinsa sosai, daga fam miliyan £30 zuwa miliyan £10.

Korar Ten Hag

Shi ma kocin Manchester United, Erik Ten Hag yana tsaka mai wuya yayin da kulob ɗinsa ke mataki na 14 a teburin Firimiya, kuma ba ya nuna alamun taɓuka komai a bana.

Wannan ya sa an fara raɗe-raɗin korar kocin wanda ya kashe kusan fam miliyan £200 kan sayo 'yan wasa zuwa yanzu, amma babu wani babban canji a tagomashin ƙungiyarsa.

Cikin waɗanda ake tunanin Man U tana dubawa, akwai tsohon kocin Borussia Dortmund, Edin Terzic, wanda ya bar kulob ɗinsa na Jamus bayan ya kai su wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai a kakar bara.

Jaridar The Sun ta Burtaniya ta yi iƙirarin cewa Terzic yana cikin waɗanda ake saka ran za su maye gurbin Ten Hag. Sannan akwai tsaffin kociyoyin Chelsea, Thomas Tuchel da Graham Potter, baya ga Zinedine Zidane, tsohon kocin Real Madrid.

A wannan yanayi dai, za a jira ganin ya za ta kaya a wasan Manchester United na gaba tare da Brentford ranar Asabar 19 ga Oktoba, don ganin ƙwazon da Ten Hag zai nuna don zai rage tararrabin korar sa.

Man United dai ba ta yi nasara ko ɗaya ba a wasanninta biyar na baya-bayan nan cikin duka gasanni.

TRT Afrika