Manchester United ta ga ci ta ga rashi a karawarsu da Sevilla FC, a zagayen kusa da na karshe na cin Kofin Europa.
Man U ta ci kwallaye biyu tun a minti 21 na farkon wasan, amma a cikin minti takwas na karshen wasan, sai ‘yan wasanta biyu, Tyrell Malacia da Harry Maguire suka ci gida, aka tashi 2 da 2.
Wasan da aka buga a Old Trafford, wasa ne tsakanin sa’anni, duk da dai Sevilla ne kulob din da ya fi kowa a duniya cin Kofin na Europa, domin kuwa ya daga kofin har sau shida.
Su kuwa Man U, sau daya tal suka daga kofin a kakar wasa ta 2017, karkashin shugabancin Jose Mourinho.
Dan wasan United dan asalin kasar Austria, Marcel Sabitzer wanda aka aro shi daga Bayern Munich ta Jamus, shi ya zuba kwallayen biyu cikin mintina takwas, a minti na 14 da minta na 21.
Amma kamar a mafarki, sai murnar Man U da burin kociyanta Erik ten Hag na cin kofi a gasar Turai, suka kwaranye, sakamakon kurakurai har sau biyu na ‘yan wasa biyu na United.
Kwallon farko dan wasan Sevilla Jesus Navas ne ya doko ta, amma ta bugi bayan Malacia ta shige ragar United. Kwallo ta biyu kuwa, El Nesyri ne ya sa mata kai sai ta doki Maguire sannan ta afka ragar United.
Dan wasan baya Harry Maguire ya yi kaurin suna wajen tafka kuskure a aikinsa na tsaron baya, wanda yakan janyo a ci ragar kulob dinsa. Hasali ma, Kociya Ten Hag ya sha benca Maguire, inda yake maye shi da Raphael Varane.
Man U dai ta kare wasan da ‘yan wasa 10, sakamakon raunin da Martinez ya samu a mintunan karshe, bayan da Ten Hag ya riga ya kammala yin canjinsa.
Yayin da za a jira zango na biyu na wasan a Alhamis mai zuwa don ganin ko waye tsakanin United da Sevilla zai zarce gaba, masu sharhi kan wasanni suna ganin cewa Sevilla za ta yi nasara a karshe.