Dan wasan Poland din ya ba da gudumawa wajen nasarar da Barcelona ta samu a wasan:Hoto/GettyImages

Dan wasan gaban Barcelona Robert Lewandowski ya ji rauni a idon sawunsa na hagu bayan ya fita daga wasa yayin wasansu na ranar Laraba da kungiyar Porto, kamar yadda kungiyar ta bayyana.

"Bayan gwaje-gwajen da aka yi da safe sun nuna cewa Robert Lewandowski ya ji rauni a idon sawunsa na hagu," kamar yadda kungiyar ta bayyana a sanarwar da ta fitar ranar Alhamis. "Zai yi jinya kuma dawowarsa ta ta'allaka ne kan warkewarsa."

Lewandowski ya ji rauni ne a minti na 21 da fara wasa. Ya so ya ci gaba da wasan, amma sai Ferran Torres ya sauya shi a minti na 34.

Barcelona ce ta yi nasara da ci 1-0 a wasan. Dan wasan Poland din ya zura ƙwallaye shida a raga kuma ya taimaka wajen zura wasu ƙwallaye hudu a wasanni 10 a kakar bana.

TRT Afrika