Ƙungiyoyi ƙwallon kafa kamar Real Madrid da Paris St-Germain da kuma Liverpool sun nuna sha'awarsu ta zawarcin Yoro, wanda ya fara taka leda a ƙulob din Lille tun yana ɗan shekara 16.  / Hoto: shafin Man Untd

Manchester United ta sayi ɗan wasan baya na Faransa Leny daga ƙulob ɗin Lille a kan kuɗin yuro miliyan 62 (£52.18m) da kuma ƙarin yuro miliyan takwas (£6.73m) a gaba.

Ɗan wasan ya rattaba hannu kan kwantiragin har zuwa watan Yuni 2029, tare da zaɓin tsawaita yarjejeniyar har tsawon shekara guda.

''Manchester United ta yi farin cikin tabbatar da cewa Leny Yoro ya koma ƙungiyar, bayan yarjejeniyar da aka cimma,'' a cewar saƙon da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na intanet.

Yaro ya buga wasanni 60 na ruƙunin farko a kulob ɗin Lille OSC tun yana ɗan shekara 18.

A kakar wasan da ya wuce, an ba shi matsayin lamba ɗaya bayan taimaka wa ƙulob ɗinsa da ya yi zuwa matsayi na huɗu a gasar wasan da aka ɓuga.

Kazalika ƙungiyoyi kamar Real Madrid da Paris St-Germain da kuma Liverpool sun nuna sha'awarsu ta zawarcin Yoro, wanda ya fara taka leda a ƙulob din Lille tun yana ɗan shekara 16.

"Rattaba hannu da na yi a kulob mai ƙima da daraja kamar Manchester United da wuri a fagen sana'ata babban abin alfahari ne,'' in ji Lny Yaro.

"Tun daga lokacin da na fara tattaunawa da ƙulob ɗin, suka fayyace min tsare-tsarensu kan yadda zan samu ci gaba a Man Utd a matsayin wani bangare na wannan aiki mai cike da shauƙi, kana sun nuna kulawa a gare ni da iyalina,'' kamar yadda Yaro ya shaida wa manema labarai.

"Na san tarihin matasan 'yan wasa a Man U kuma ina da yaƙinin kulob ɗin zai iya zama wuri mafi kyau a gare ni don cimma burina, tare da sabbin abokan wasana. Na zaƙu na fara aiki," in ji shi.

Dan Ashworth, daraktan wasanni na Manchester United, ya ce: "Leny yana ɗaya daga cikin matasan 'yan wasa masu ƙayatarwa a fagen ƙwallon kafa a duniya.

"Sannan ya mallaki dukkan siffofin da ake buƙata don samun ci gaba a ɗan wasa, la'akari da cewa yana da tarihi mai kyau a rayuwarsa ta ƙwallon kafa, muna farin cikin tallafa masa don cimma burinsa a nan Manchester United.

''Wannan kulob ɗin ya kafa tarihi mai kyau wajen inganta matasan 'yan wasa, kama daga 'yan cikin gida ko kuma waɗanda aka sayo daga waje, tare da ba su jagorancin da ake bukata.

A karkashin jagorancin Erik ten Hag da ƙwararrun ma'aikatanmu, za mu tabbatar da cewa Leny ya samu damar cim ma nasarar da kowa a cikin ƙungiyar ke burin samu," in ji Dan Ashworth.

AFP