Rahotanni sun ce kungiyar kwallon kafa ta Al Hilal da ke Saudiyya ta yi tayin sayen dan wasan gaban Paris St-Germain Kylian Mbappe a kan €300m wato (£259m).
Kamar watsa labarai ta Press Association ce ta rawaito wannan labari.
Dan kasar Faransa mai shekara 24 na da sauran shekara daya kafin kwangilarsa ta kare a PSG kuma kawo yanzu ya ki sanya hannu domin tsawaita zamansa a kungiyar.
Yanzu dai PSG tana son sayar da Mbappe maimakon barinsa ya tafi salin-alin a bazara mai zuwa.
Hasalima kungiyar ta ki sanya shi a cikin tawagar da za ta tafi Japan da Koriya ta Kudu domin murza leda.
A shekarar 2017 PSG ta sayi Neymar daga Barcelona a kan £200m.
Rahotanni sun ce kungiyoyi irin su Tottenham, Chelsea, Man United, Inter Milan da Barcelona suna son daukar dan wasan.
Mbappe ya ce yana so ya ci gaba da zama a PSG har nan da shekara daya lokacin da kwangilarsa za ta kare. An yi amannar cewa yana son tafiya Real Madrid.