Dan wasan Maroko Achraf Hakimi ya barar da bugun durme a minti 85 na wasan. Photo: AFP

Kocin Maroko Walid Regragui ya ce ya dauki dukkan alhaki game da fitar da kasar da aka yi daga gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka, a matakin 'yan-16. A daren Talata ne Afirka ta Kudu ta doke Maroko da ci 2-0.

Tagawar Maroko da ake wa lakabi da "Zakunan Atlas", suna cikin wadanda aka yi wa zaton lashe kofin a bana. Sai ga shi sun zamo cikin manyan kasashe da aka fitar daga gasar bayan wasansu a filin wasa na Laurent Pokou da ke San Pedro, a Ivory Coast.

Dan wasan Afirka ta Kudu, Evidence Makgopa ne ya zura kwallo a minti na 57, inda daga bisani Teboho Mokoena ya zura ta biyu a mintunan karshe na wasan, daga bugun tazara, sakamako laifin da dan wasan Maroko Sofyan Amrabat ya yi har aka ba shi jan kati.

Kocin na Maroko, Regragui ya fada wa beIN Sports cewa, "Da za mu iya cin wasan tun a rabin farko na wasan, amma a irin wannan mataki mun barar da damarmaki".

Babbar dama

Maroko ta samu babbar damar rama kwallon farko, ana minti biyar ya rage a wasan, lokacin da aka ba su bugun durme, amma sai Achraf Hakimi ya barar da damar inda kwallon da ya buga ta bugi turken raga.

Regragui ya bayyana cewa, "Bugun da muka barar ya mana ciwo, haka kuma ba mu yi kokarin da ya kamata ba, amma na amsa duka wani alhakin abin da ya faru".

Maroko dai ta yi burin cin kofin kwallon kafa na Afirka a bana, wan rabonta da ci tun shekarar 1976, sakamakon kokarin da ta nuna a gasar Kofin Duniya na 2022, inda Maroko ta zamo kasar Afirka ta farko da ta kai matakin gab da na karshe.

Sai dai kuma, kokarin maroko a gasar AFCON da ake a Ivory Coast babu wani armashi, sannan rashin wasu manyan 'yan wasa a wasan nasu da Afirka ta Kudu, kamar Hakim Ziyech da Sofiane Boufal ya kawo musu cikas.

Regragui ya kara da cewa, "Za mu dauki darasi daga wannan matsala da muka samu, mun san abin nan ya kona wa masoyanmu rai, wadanda sun ba mu goyon baya matuka".

TRT Afrika