Dan wasan Maroko El Bakkali ya lashe Kofin Duniya a wasan tsere na mita 3,000 na maza

Dan wasan Maroko El Bakkali ya lashe Kofin Duniya a wasan tsere na mita 3,000 na maza

Soufiane El Bakkali ya lashe kofin duniya karo na biyu a jere a wasan tseren mita 3,000 na maza.
Dan wasan Maroko Soufiane El Bakkali ya zo na daya a wasan tseren karshe na maza na tsawon mita 3000 da aka yi. Hoto: AA

Dan wasan kasar Maroko Soufiane El Bakkali ya lashe lambar yabo ta zinare a gasar Olympics, kazalika ya lashe gasar cin kofin duniya karo na biyu a jere a gasar tseren mita 3,000 ta maza a ranar Talata.

Dan wasan, mai shekaru 27, ya yi nasarar lashe gasar cikin minti takwas da dakika 3.53, inda ya kwace kambun gasar ta duniya daga hannun mai rike da ita sannan wanda ya lashe lambar yabo ta azurfa a gasar Olympic, Lamecha Girma dan kasar Habasha.

"Bayan nasarar da na samu ta lashe gasar a bara, ina alfahari da sake dawowa da wata lambar yabo ta zinare," cewar El Bakkali.

“Na shirya wa wannan gasa sosai, sai dai filin na yau ya hada jajirtattun ‘yan wasa kamar Lamecha da sauransu.

"Na zo cikin shiri da tabbacin cewa zan iya samun nasara. Wannan lambar yabo ta kara min kwarin gwiwa a gasar Olympics da za a yi a birnin Paris, ina son na kara yin nasara a can ma." in ji El Bakkali.

Girma, mai shekaru 22, wanda ya yi nasara a mintuna 7:52.11 a gasar Diamond League ta Paris da aka yi a ranar ranar 9 ga watan Yuni, ya yi rasa tarihin da ya kafa na riko da kambun gasar ta shekaru 19 a duniya bayan da El Bakkail ya doke shi a wasan tseren karshe na tsallen ruwa a kokarinsa na samun lambar azurfa ta uku a duniya cikin mintoci 8:05.44.

Karfin gwiwa

"Na gamsu da duk tseren da na yi da El Bakkali," in ji Girma. Ya kara da cewa "Har yanzu ina burin lashe kambun zinare a gasar cin kofin duniya ko na Olympics. Babu abin da ya canja a burina da na sa a gaba, in ji shi

"Watakila hakan zai kara min himma a shekara mai zuwa. A kowane yanayi, zan ci gaba da kokari da na saba don lashe zinare na duniya."

A wasan karshe da aka yi, dan wasan Kenya Abraham Kibiwot ya bugu da wani shinge da ya yi sanadin faduwarsa, amma duk da hakan bai karaya ba, ya yi sauri tashi ya koma kan kafafunsa ya kuma zarce abokin wasansa Leonard Kipkemoi Bett, hakan ya sa ya yi nasarar samun lambaryabo ta tagulla da cikin mintuna 8:11.98.

"Wannan ne karo na farko da na samu lambar yabo a gasar cin kofin duniya, na zo nan ne domin na iya samun wani lambar yabo da zan koma da shi ni gida a karshe," a cewar Kibiwot.

"Gasa ce mai kyau - duk da cewa na fadi a lokacin da muka zo matakin karshe na gasar, ba don haka ba, da na iya kai wa zuwa ga makin karshe na wasan.

"Amma a wannan lokacin babu wata gajiya. Na ji dadi sosai, abun da na samu ya sa ni farin ciki mara misaltuwa."

TRT Afrika