Manchester United tana mataki na 12 a teburin gasar Europa, da maki 9 daga wasanni 5. / Hoto: Reuters

Bayan jagorantar Manchester United a wasanni biyu tun bayan karɓar ragamar ƙungiyar, koci Ruben Amorim ya amsa cewa yakan shiga tararrabi yayin da yake kallon 'yan wasan a filin wasa.

Kocin ya faɗi hakan ne yana mai kokawa kan rashin iya riƙe ƙwallo da 'yan wasansa suke yi, bayan da suka yi nasara a wasan da suka buga da Bodo/Glimt ranar Alhamis a Gasar ta Europa League.

Amorim ya samu nasara a karon farko da Manchester United, bayan da suka tashi 3-2 a filin wasansu na Old Trafford. A wasan farko da Amorin ya jagoranta, United ta yi canjaras da ci 1-1 ne tare da Ipswicth a gasar Firimiya ranar 24 ga Nuwamba.

A wasan na biyu, Alejandro Garnacho ne ya fara ciyo wa United ƙwallo, kafin da Bodo/Glimt su farke kuma su ƙara ƙwallo ta biyu.

Sai dai Rasmus Hojlund ya rama ƙwallo kuma ya ƙara ta uku, wadda ta bai wa United nasara a wasan na mako na 5 a gasar Europa.

Rashin tabbas

Da aka tambaye shi game da wasan, Amorim ya faɗa wa TNT Sports cewa, "Mun fara da sa'a, amma sai aka sha mu ƙwallaye biyu. Na ji daɗin yadda 'yan wasan suka taka leda."

Kocin ya amsa cewa yakan shiga tararrabi kafin fara wasa saboda rashin tabbas a ƙwazon tawagarsa. Ya ce, "Nakan shiga damuwa saboda ban san abin da zai faru ba."

"Ban gama sanin 'yan wasana ba, kuma ba mu daɗe muna aiki tare ba. Mukan shiga wasa da karsashi, amma a lokaci guda kakan ji karaya saboda ba ka san yadda wasa zai kasance ba."

Duk da cewa nasarar ta bai wa Ruben Amorim ƙwarin gwiwa, amsa cewa yana samun fargaba alama ce ta girman ƙalubalen da yake fuskanta a Manchester United.

Ranar Lahadi United za ta karɓi baƙuncin Everton a Gasar Firimiya, inda kocin zai yi ƙoƙarin tabbatar da ɗorewar nasararsa a ƙungiyar da a yanzu take mataki na 12 a gasar bayan wasanni 12, da maki 16.

TRT Afrika