Xavi  ya jagoranci kungiyar wajen lashe kofin Sifaniya a kakar wasa ta 2022-23, sai dai kashin da suka sha a hannun Villareal da ci 5-3 ranar Asabar ya sa suna bayan Real Madrid da maki 10. / Hoto: Reuters

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Xavi ya ce zai ajiye aikinsa a karshen kakar wasan da muke ciki.

Tsohon dan wasan na Barcelona da Sifaniya ya soma aiki ne a watan Nuwamba na 2021 bayan ya bar kungiyar Al Sadd ta kasar Qatar.

Ya jagoranci kungiyar wajen lashe kofin Sifaniya a kakar wasa ta 2022-23, sai dai kashin da suka sha a hannun Villareal da ci 5-3 ranar Asabar ya sa suna bayan Real Madrid da maki 10.

"Ina ganin ya kamata a samu sauyi. Ba zan bar wannan yanayi ya tabarbare ba," in ji Xavi mai shekara 44.

Xavi, wanda ya lashe kyautuka 25 a zamanin da ya murza leda a Barcelona, zai sauka daga kan mukaminsa ranar 30 ga watan Yuni duk da cewa kwantaraginsa ba ta kare ba.

TRT Afrika